A jawabin da shugaban Kasa Muhammadu Buhari yayi ranar murnar cika shekaru 61 da samun ‘yancin kai ya bayyana cewa gwamnatin sa ta bada umarnin a rika daukar sabbin ‘yan sanda 10,000 duk shekara a kasar har sai an shekara 6 ana haka.
Buhari ya yi wannan alkawari domin kawo karshen rashin tsaro da ake fama da shi a kasar.
Idan ba a manta ba wasu kwararru a fannin samar da tsaro sun koka kan karancin jami’ai da rundunar ‘yan sandan kasar nan ke fama da shi.
A kwanakin baya sifeto-janar din ‘yan sandan Najeriya, Usman Alkali ya bayyana cewa nan ba da dadewa ba hukumar za ta fara daukar sabbin jami’ai har 20,000.
Discussion about this post