Gwamna Bello Masari na Jihar Katsina ya nuna matuƙar damuwa dangane da yadda masu shari’a da kotuna ke sakin ‘yan bindiga, masu fyaɗe da sauran masu aikata muggan laifuka da sunan beli.
Masari ya nuna wannan damuwar jim kaɗan bayan ya rantsar da sabbin alƙalan manyan kotuna guda uku na Jihar Katsina.
Daga nan sai ya yi kira ga Ƙungiyar Lauyoyi ta Najeriya cewa ta ja kunnen mambobin ta, su daina fakewa da ‘yancin ɗan Adam su na ɗaure wa muggan masu laifi gindi ana sakin su.
“Mu na cikin yanayi na babbar matsalar tsaro cike da barazana. Don haka tilas sai mun haɗa kai wuri ɗaya, domin magance waɗannan ƙalubale.”
“Mun sha samun rahoto ko ganin yadda aka bada belin ‘yan bindiga, ‘yan fashi da makami da masu aikata fyaɗe, amma daga baya kuma su sake aikata laifin da su ka yi aka karɓi belin su.
“Irin wannan mummunar ta’asa ai da ba a bada belin su ba, ba za su sake samu damar maimaita irin ta ba.” Inji Masari.
Ya kuma yi kiran da a riƙa gaggauta yanke hukunci ana yi wa mai gaskiya adalci.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda ɓangarorin shari’a ke nuna juna da yatsa, su na ɗora wa juna laifin matsalolin da ke dabaibaye shari’u.
Ya kuma umarci kwamitin da ya kafa cewa su binciki mummunar halayyar yadda ake yawan sakin masu aikata fashi, ‘yan bindiga da masu aikata fyaɗe da sunan wai an bada belin su.
Daga nan ya ce sabbin Manyan Alƙalan Babbar Kotu ɗin da ya naɗa su ɗauki aikin da aka ɗora masu a matsayin damar jajircewa su yi aiki tuƙuru, tare da nuna kishi.
Discussion about this post