Biyo bayan fara amfani da sabuwar dokar harkokin man fetur a Najeriya, wadda ta ƙirƙiri sabbin hukumomin fetur biyu kwanan baya, Gwamnatin Tarayya ta rushe Hukumar Rarraba Man Fetur (DPR) da Hukumar Yanka Farashin Litar Fetur (PPPRA), sai kuma Hukumar Kula da Gidauniyar Kuɗaɗen Fetur (PEF).
Sabuwar dokar harkokin man fetur ce ta tanaji sharuɗɗa da umarnin rushe hukumomin guda uku.
An maye gurbin hukumomin uku da NPRA da kuma NURC.
Ƙaramin Ministan Harkokin Fetur, Timipre Sylva ne ya sanar da rushe hukumomin, tare da cewa sabbin hukumomin da dokar ta kafa, wato NPRA da NURC sun fara aiki tun a ranar Litinin.
Ya ce za a ci gaba da aiki tare da dukkan ma’aikatan hukumomin uku da aka rushe.
“Dokar da ta rushe hukumomin uku ta kare dukkan ma’aikatan hukumomin, wato babu wanda za a sallama ko da mutum ɗaya.
“Amma fa dokar ba ta bada kariya ga shugabannin hukumomi ukun da aka rushe ba, domin su dama naɗi ne na siyasa, ba ma’aikatan gwamnati ba ne.”
Don haka Sylva ya ce dukkan ma’aikatan NPRA da NURC za su fito ne daga hukumomin da aka rushe guda uku na DPR, PPPRA da PEF.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda wasu makusantan Shugaba Muhammadu Buhari ke ƙoƙarin riƙe maƙogaron harkokin haƙo fetur a ƙasar nan, ta hanyar yin katsalandan a naɗin ssbbin shugabannin NPRA da NURC.