Gagarimar matsalar tsaron da ta dabaibaye Najeriya tare da dagula tattalin arzikin ƙasar, kusan ita ce babban dalilin da ya sa ake yawan ciwo basussuka domin cike giɓin da ake samu a Kasafin Kuɗaɗe.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe Zainab Ahmed ce ta bayyana haka.
A kasafin 2022 dai Najeriya na sa ran za ta samu kuɗin shiga naira tiriliyan 10, yayin da ta kasafta kashe Naira miliyan tiriliyan 16.
Wannan ya na nufin an samu giɓi kenan har na Naira tiriliyan 6, waɗanda Najeriya ta ce za ta cike sauran tiriliyan 6 ɗin.
Ko a kasafin 2021 sai da aka samu giɓi wawakeken giɓi na Naira tiriliyan 5.2.
Yayin da ake fama da wannan yawan ciwo bashi, a gefe ɗaya kuma bashin sai ƙara yawa ya ke yi.
Yadda bashin ke ƙara yawa, haka ita matsalar tsaro ke ƙara muni a faɗin ƙasar nan.
Premium Times Hausa ta buga labarin yadda Sanata Lawan ya damu da wawakeken giɓin da aka samu.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan, ya nuna damuwar yadda ake ta samun wawakeken giɓi a kasafin Najeriya, musamman na 2022.
Ya yi wannan ƙorafin a ranar Alhamis, lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da Kasafin 2023 a Majalisa.
An dai samu giɓin zunzurutun Naira tiriliyan 6.26, waɗanda Buhari ya ce duk bashi za a rakito domin a cike giɓin.
Lawan ya ce yawan giɓin akwai abin dubawa sosai a ciki, don haka Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya za su bi kasafin filla-filla domin a yi masa aski, sasabe da kwaskwarimar rage wasu kuɗaɗe, ta yadda Najeriya za ta yi kasafin da zai zama daidai ƙarfin aljihun ta, da kuma daidai ƙarfin wuyan da zai iya ɗaukar bashin da za a ciwo.
“Babbar matsalar da ke addabar kasafin kuɗi a Najeriya ita ce matsalar yadda za a karɓi haraji da kuma ta yadda harajin ke shiga aljihun gwamnati.
A lokacin gabatar da kasafin, Buhari ya yi magana kan masu nuna damuwa da yawan bashin da ake ciwowa.
“Duk mai tantamar bashin da mu ke ciwowa ya je kawar da shakku a kan mu.”
Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bashin da gwamnatin sa ke ciwowa bai kumbura cikin da zai rikita ƙasar nan ba.
Ya ce ayyukan da ake yi da kudaden da ake ciwowa bashi a bayyane su ke, don haka duk mai tantama zai iya fita ya yi bincike ya gani da kan sa.
Buhari ya yi wannan kalami a gaban gamayyar Sanatoci da Mambobin Majalisar Dattawa, yayin da ya ke gabatar masu da kasafin 2022 na Naira tiriliyan 16.39.
A cikin kasafin dai ya bayyana cewa Naira tiriliyan 4.11 za a kashe su wajen biyan albashi da sauran haƙƙin tafiyar da ma’aikatan gwamnati.
Sai kuma zunzurutun Naira tiriliyan 3.61 waɗanda za su tafi wajen biyan basussukan baya, wanda gwamnati ke yi a kowane ƙarshen wata.
Buhari ya ce za a kashe Naira biliyan 579 wajen biyan haƙƙin ‘yan fansho da biyan garatuti.
Yayin da Buhari ke jawabi, ya yi bitar wasu muhimman ayyukan da gwamnatin sa ta yi a shekarar da ta gabata, sannan kuma ya jinjina wa kan sa bisa ƙoƙarin da ya yi na tsayuwar sama da minti 50 ya na jawabi wajen gabatar da kasafin 2020. Kuma ya ce a wannan ranar ma zai yi bajintar sake yin irin waccan tsayuwar.