Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana cewa ta fatattaki wasu ‘yan ta’adda waɗanda su ka yi yunƙurin kai wa sansanin tubabbun Boko Haram hari.
Kakakin Sojojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ya ce ‘yan ta’addar Boko Haram ɓangaren ISWAP ne su ka nemi kai harin a ranar Lahadi.
Ya ce an yi yunƙurin ne a sansanin tubabbun ‘yan Boko Haram da ke Karamar Hukumar Damboa ta Jihar Borno. Amma an Sojojin Najeriya sun nuna masu sun fi ƙarfin su, kuma sun fi su ƙarfin makamai.
An kai wannan hari a lokacin da Boko Haram ke ta tururuwar yin saranda su ka ajiye makamai.
Yanzu haka dubban ‘yan Boko Haram da su ka haɗa da iyalan su, sun yi saranda, kuma su na ƙarƙashin kulawar Gwamnantin Tarayya.
Shugaba Buhari a jawabin sa na murnar cikar Najeriya 61 da samun ‘yan, ya ce akwai Boko Haram kamar mutum 8,000 da su ka yi saranda.
Wanann hari dai zai iya kasancewa wani yunƙuri ne ‘yan ta’adda su ka yi, domin sare guyawun ‘yan’uwan su maso ajiye makamai.