Tsohon sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya yi kira ga masu son zama shugaban kasa a Najeriya su fito su nuna kan su su dai kururuwa a bayan fage sannan su ba fitowa suka yi suka ce suna so.
Sarki Sanusi ya bayyana haka ne a hira da yayi da talbijin din Arise, lokacin da yake amsa tambayar da maigabatar da shirin, tsohon kakakin shugaban Kasa Goodluck Jonathan rueben Abati ya yi masa game da tsarin karba-karba.
” Wasu daga cikin gwamnonin yankin Arewa sun ce yankin ce za ta yi shugaban kasa, gwamnonin Kudu suma sun ce sune suke so. dole sai dan yankin ne zai zama shugaban kasa. Akwai dokokin kasashe a duniya da suka amince da mulkin karba-karba, idan haka muke so a Najeriya sai mu saka haka a kundin tsarin kasa. Amma idan babu bai zama kuma dole a rika fitowa ana cewa wai dole idan wancan bangaren yayi sai kuma a maida wata sashen kasar.
Muhammadu Sanusi ya ce masu so su fito su nuna kansu musan su mu zabi wanda muka ga ya fi dacewa.
” Irin haka ne ba za a fito su nuna fuskokin su ba sai lokaci ya kure jam’iyyu su fiddo mana tarkace sannan a ce mana sune ‘yan takarar dole mu zabe su don babu abin yi. Amma tun yanzu su nun fuskokin su mu san inda muka dosa, in yi yi, in bari bari idan a canja ne ma sai a canja.
Discussion about this post