Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kirkiro sabbin manyan makarantun gaba da sakandare a jihar Jigawa.
Wadannan makarantu da shugaba Buhari ya saka hannun kirkirar su sun hada sa Kwalejin koyan ayyukan Noma na gwammantin tarraya a Kirikassamma, da kuma Kwalejin Ilimi ta tarayya a garin Birnin Kudu.
Kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ne ya fidda wannan sanarawa ranar Juma’a.
Bayan haka shugaban Buhari ya saka hannu a cibiyar binciken ayyukan gona ta Kasa dake gaban sa.