Shugaba Muhammadu Buhari ya shafe lokaci mai tsawo ya na yi wa Najeriya addu’ar samun zaman lafiya da kawo karshen matsalar tsaro a ƙasar nan, a Masallacin Madina.
Masallacin Madina a can ne kabarin Annabi Muhammadu (SAW) da na matar sa ɗaya, A’isha (RA) su ke.
A ciki ne kuma ƙaburburan Sahabbai biyu Abubakar, Umar (RA) su ke.
Shi ne masallaci na biyu a daraja a duniya. Daga Ka’aba sai shi na Madina ɗin.
Kakakin Yaɗa Labaran Shugaban Ƙasa, Garba Shehu ya sanar a cikin wata takardar da ya fitar cewa bayan kammala taron masu zuba jari, Buhari da ‘yan rakiyar sa sun zarce Madina domin ziyara Masallacin Manzo (SAW), inda ya ɗauki tsawon lokaci ya na yi wa Najeriya da duniya addu’ar zaman lafiya.
“Haka kuma Shugaba Buhari ya shafe lokaci ya na karatun Alƙur’ani a cikin Masallacin.” Inji sanarwar Garba Shehu.
“Daga Madina kuma Buhari zai zarce Makka inda zai je ya yi Umrah.”
Sanarwar dai ba ta bayyana sunayen ‘yan rakiyar Buhari zuwa Makka da Madina ba, amma dai daga cikin su akwai na daga gaba, Ministan Sadarwa, Isa Pantami.
PREMIUM TIMES Hausa ta ga hotunan hamshaƙan attajiran Najeriya, Aliko Ɗangote, Abdulsamad Rabiu da Ɗahiru Mangal a cikin kayan harami, wanda ke nuna cewa duk a lokaci ɗaya su ke da Buhari.
Dama kuma su ukun sun halarci taron masu zuba jarin wanda aka shirya a Saudiyya.
Nan a gida kuwa, shi ma Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya jagoranci manyan limaman Kiristoci n Najeriya sun yi addu’o’in samun zaman lafiya a Najeriya.
Discussion about this post