Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada halin sa da ya daɗe ya na nunawa, inda wannan karo ma ya ce ayyukan da gwamnatin sa ta yi wa Najeriya sun zarce na dukkan shugabannin da aka yi tun daga 1999 zuwa yau.
Buhari na magana ce a kan gwamnatocin Obasanjo, Umaru ‘Yar’Adua da Goodluck Jonathan.
Ya yi wannan iƙirarin e a cikin jawabin sa na murnar cikar Najeriya 61 da samun ‘yanci a ranar Juma’a.
Sai dai kuma sahihan hujjojin ayyukan da aka yi a ƙasa sun nuna babu ƙamshin gaskiya a jawabin na Buhari.
“Babu gwamnatin da ta yi aikin da mu ka yi a cikin shekaru shida tun daga 1999 zuwa yau.” Haka ya furta a cikin jawabin.
Duk Da Buhari Ya Yi Bakinta A Wasu Fannoni, Akwai Inda Bai Taɓuka Ba:
Gwamnatin Buhari ba ta taɓuka ba fannin inganta tattalin arziki, fannin tsaro, fannin inganta ilmi da kiwon lafiya.
Haka kuma a fannin yaƙi da cin hanci da rashawa, babu wani ƙoƙarin da gwamnatin Buhari ta yi fiye da na gwamnatocin Obasanjo, Umaru da Goodluck Jonathan.
Matalauta da masu fama da ƙuncin rayuwa sun fi yawa a yanzu fiye da shekarun baya kafin Buhari ya hau a 2015.
Sannan gwamnatin sa ta shiga ruguguwar rashin iya ayyuka da almubazzarantar da dukiya.
Haka a ɓangaren adawa, yayin da aka kafa APC a kan mayafin bajau ɗin adawa, bayan Buhari ya hau mulki sai gwamnatin sa ta fi ta Obasanjo da Umaru da Jonathan yaƙi da nasu adawa da gwamnati.
Tsadar Kayan Abinci Lokacin Da Gwamnati Ke Barka Kuɗi A Fannin Noma:
Duk cewa a kullum talakawa na jin labarin irin maƙudan kuɗaɗen da gwamnati ke narkarwa a fannin bunƙasa noma, tsadar abinci sai ci gaba ta ke yi da kassara masu ƙaramin ƙarfi a ƙasar nan.
Kusan farashin komai na abinci ya nunka daga hawan Buhari a 2015 zuwa yau.
Miliyoyin jama’a na zargin cewa kuɗaɗen da ake warewa domin bunƙasa noma, ba su zuwa hannun waɗanda ake ware kuɗaɗen don su. Kuma har yau ba a kama ko mutum ɗaya da laifi ba.
Matsalar Tsaro: Shugaban da aka zaɓa saboda ya na ta bugun ƙirji da kirarin zai iya magance matsalar tsaro cikin ƙanƙanen lakaci, sai ga shi jihar sa ta afka cikin mummunan halin da ba ta taɓa samun kan ta ba a tarihin kafuwar Najeriya.
A kan idon sa ‘yan bindiga sun kafa ‘dauloli’ a Katsina, Zamfara, Sokoto, Neja, Kaduna da wasu sassa.
Har yanzu Boko Haram na cin kasuwa a Arewa maso Gabas. Kuma shirin gwamnatin sa na yafe wa ‘yan ta’adda ana ba su jarin kama sana’a, kusan abu ne da akasarin ‘yan Najeriya ba su yi murna da shi ba.
A ƙarƙashin mulkin Buhari kusan babu jihar da ba a cikin tashin hankali a ƙasar nan, sai wasu ‘yan tsiraru.
A lissafin munin ta’addanci a duniya, Najeriya ce ƙasa ta uku, a lissafin da aka yi na cikin 2017.
A ƙarƙashin gwamnantin Buhari ‘yan tada ƙayar baya masu neman ɓallewa a Najeriya sun ƙara bayyana sosai. Kuma ƙabilanci da ɓangaranci ya ƙara ruruwa.
A ɓangaren cinikayya a ƙasashen waje kuwa, yawancin farashin kaya a ƙasashen ƙetare bai canja ba tun daga 2015 zuwa yau. Amma kayan da ka sayo a dala miliyan 1 shekaru huɗu baya, idan Naira miliyan 200 ka canji dala, to a yanzu sai ka canje ta fiye da Naira miliyan 400.
Wannan shi ne irin ci gaban da aka samu daga 2015 zuwa yau.
Discussion about this post