Stella Oduah ba boyayya bace a Najeriya musamman idan batu ake na tafka harkalla da wafce kuɗaden gwamnati.
Abu ɗaya kawai da zaka yi mata, ta kuma nuna halinta shine ka naɗa ta muƙami, za ta ko nuna maka cewa ta kware a harkallar cika aljifai da kuɗaɗen amana da aka sanya su a ƙarƙashin ta.
An naɗa Oduah ministar sufurin jiragen sama daga shekarar 2011 zuwa 2014. Sai dai kuma ko a lokacin ba ayi rabuwar arziki ba. Shugaban kasa a wancan lokaci bayan an banƙado wasu harkalla da ta tattafka korar ta yayi daga kujerar minista.
Saboda tsananin basussukan da ta cicciyo daga bankunan ƙasar nan, kotu ta umarci a kwace ƙadarorinta. Sai dai kuma akwai wasu manyan gidajenta guda hudu wanda ta siye su a birnin Landan wanda su sun sha domin har yanzu suna nan mallakinta ne.
Ɗaya daga ciki da sunanta ta siye shi, biyu kuma da sunan wani kamfaninta da ta yi rajistar sa a Najeriya.
Oduah wacce sanata ce a Najeriya ta canja sheka da PDP zuwa APC a cikin watan jiya, jam’iyyar da masu fashin baki ke cewa jam’iyyar da duk harkallar ka idan ka shige ka tsira.
Sanatar ta yi amfani da wani kamfanin tsibirin Seychelles, wanda wannan tsibiri wuri ne da ake dasa harkalla hankali kwance ba tare da wani ya ce maka ci kanka ba.
Ta hanyar wannan kamfani da ta rika loda wa kuɗaɗe masu yawa ta siya manyan gidaje a Landan guda hudu da aka yi musu kuɗi a jimlace dukkan su hudun suka tashi kan Fan miliyan 6.7 a tsakanin watan Oktoban 2012 da Agustan 2013.
A lissafe dai yanzu kuɗin gidajen duka huɗu sun tashi akan naira biliyan 5.2, idan aka duba darajar Fan 1 da ya kai naira 775 a kasuwar bayan fage kenan. Idan kuma lissafin ka akan musayar canjin na CBN ne, ₦558, to gidajen zasu tashi akan naira biliyan ₦3.7.
An bankaɗo wannan harkalla ne a wata gagarimar bincike wanda kamfaninin jaridu 150 na duniya ciki har da PREMIUM TIMES suka gudanar akan yadda hamshaƙan Najeriya da duniya suke wawushe kuɗaɗen talakawa suke jibge su a wasu ƙasashen duniya da ba a biyan haraji.
Adireshin gidajen
– Flat 2, 7 Devonshire Terrace, London (W2 3DN) da aka siya ranar 06/08/2013
Kuɗin gidan: £378,000.
– Top Floor Flat, 89 Brondesbury Villas, London (NW6 6AG) da aka siya ranar 12/08/2013
Kudin da aka sayi gidan: £369,000.
– Fourth Floor Flat, 19 Warrington Crescent, London (W9 1ED) da aka siya ranar 15/08/2013
An siya : £680,000.
Ƙarya Doka
A bisa dokar Najeriya ya haramta wani mai rike da muƙamin gwamnati ya ci gaba da zama darekta a wani kamfani na sa, yin haka karya doka ce kuma Oduah ta yi. Sannan kuma duk wani kadara da za ka mallaka sai ka bayyana yadda ka same su, ita ko Stella ko kadan ba ta yi hakan ba.