Peter Obi wanda tsohon gwamnan jihar Anambra ne kuma tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2019 kuma yayi suna matuka wajen tallata kansa a matsayin mutumin kirki wanda tsakanin sa da harkalla, babakere da handama sai dai gani daga nesa amma ba ya kai ga ya saka hannu ba.
Sannan kuma a duk lokacin da yake jawabi a wajen taro yakan rika kuranta kansa cewa shi mai gaskiya ne kuma ya samu daukaka a harkokin sa na kasuwanci da aikin gwamnati.
Za aji yana cewa shine matashi na farko da ya taba yin kafada da kafada da manyan daraktocin bankin Fidelity tun yana dan shekara 34 da sauransu da suka hada da manyan mukamai da ya rike a kamfanoni da dama da kuma hannayen jarin da yake da su a wasu kamfanonin wanda ya mallake su ta hanyoyin da suka dace, wato kamar yadda yake fadi.
Ashe duk kuri yake yi, akwai wasu abubuwan da ya boye su ba a sani a kasasshen waje daga shi sai iyalan sa.
A wannan bincike da PREMIUM TIMES ta yi ta gano cewa ashe tsohon gwamna Obi ya yi rufarufa da dama a wasu harkalla da ya tafka wanda ya boye su ya sassaka sunayen ya’yan sa, yana kwasan garabasa a wadanna kasashe da ba a biya wa kamfanoni haraji.
Wannan bincike ne da Hadaddiya Kungiyar ‘Yan jarida masu binciken Kwakwaf ta Duniya suka yi kuma suka bankado harkalla da cuwacuwa da handame handame da shugabannni da manyan kasashen duniya suka tafka a boye ba a sani ba.
Akalla ‘yan jarida 600 ne dake aiki a kamfanoni 150 suka yi wannan aiki na zakulo wadannan mutane domin duniya ta sansu sannan aka yi mata suna ‘Takardun Pandora’.
Wadannan ‘yan jarida sun tantance takardu da fayil fayil, bayanai, rahotanni da rubuce-rubuce da sauransu sama da miliyan 11.9.
Shi ma tsohon gwamna Obi na daga cikin wanda aka bankado harkallar sa a cikin wadannan bincike ta duniya da aka gudanar.
Tabbas, an gano cewa ashe gogan naka yana da wasu kamfanoni da harkallar da yake yi a boye yana jidar daloli ba a sani ba. Ya bude irin wadannan kamfanoni a kasashen waje, sannan ya boye sunan sa don kauce wa biyan haraji wanda yin haka kacokan sabawa dokokin Najeriya.
A hira da PREMIUM TIMES ta yi da shi kai tsaye ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa lallai bai bayyana wadannan kamfanoni da kadarori wa hukumomin gwamnatin Najeriya a lokacin da yake cika fom din bayyana kadarorin sa da yake neman kujerar siyasa ba saboda wai bai san ana haka bane.
Ya ce bashi da masaniyar doka ta tilasta shi ya bayyana duka kadarorinsa har da wadanda bashi kadai bane ke da mallakinsu, wadanda suke hadin guiwa ne tare da iyalan sa ko kuma wasu da ban.
An gano cewa kamfanonin da Obi ya bude ya bude su ne da sunayen ‘ya’yan sa da na mai dakinsa sannan kuma dama su kan bude irin wadannan kamfanoni ne a kasashen da aikin su shine su rika taimakawa attajirai da dakaren wasu kasashe su zo su bude kamfanoni a kasashen ba tare da suna biyan haraji ba, wato dai hanyar da zasu kauce wa dokokin kasashen su. Idan suka wafci kudaden talakawa sai su garzaya can su narka su babu mai ce musu ci kanka.
Obi ya karya dokokin Najeriya da suka hada da kauce wa biyan haraji da kuma bayyana adadin kamfanoni da kadarori da ya mallaka a lokacin da zai zama gwamna.
An gano cewa ya ci gaba da zama shugaban wasu kamfanoni na sa wasu kuma a matsayin mataimaki har bayan ya zama gwamnan jihar Anambra wanda saba wa doka ce ita ma a Najeriya.
Discussion about this post