Ɗan Majalisar Tarayya Nicolas Mutu ya fi dukkan sauran wakilan tarayya daɗewa a majalisa. Sai dai kuma banda wannan tarihi da ya kafa, Mutu ya sake kafa wani tarihin ƙadaba-ƙadaba.
Tun cikin watan Afrilu 2020 ya shiga hannun masu binciken EFCC, kuma aka gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya.
Baya ga wannan kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa ya karya dokar Najeriya, inda ya kafa kamfanin gare a tsibirin Seychelles, domin riƙa karkatar da maƙudan kuɗaɗe a can.
Tuni har wannan kamfani da Nicolas Mutu ya kafa, ya sai masa kantamemen gida a Landan na Naira Miliyan 566. Bincike ya tabbatar da haka.
Irin wannan hada-hadar kuwa dokar Najeriya ta haramta wa duk wani mai riƙe da muƙami ita.
Dokar CCB ta haramta wa ma’aikataci yin duk wata sana’a ko kasuwanci in dai ba noma kaɗai ba.
Nicolas Mutu na daga cikin ‘yan harƙallar da Binciken Pandora Papers ya fallasa, waɗanda su ka haɗa shugabanni na baya, manyan masu mulki, ‘yan siyasa da sauran masu riƙe da manyan muƙamai, alƙalai, jami’an tsaro da sauran su.
Cikin 2010 mutu ya kafa kamfani mai suna Forest Group of Company a Tsibirin Seychelles.
Cikin 2012 kamfanin ya sayi gida a Arewacin Landan na fam 620,000.00. Ya saida gidan cikin 2014 kan fam miliyan 730,000.00, kwatankwacin kusan naira miliyan 566 kenan. Wato idan za a canja duk fam 1 a kan Naira 775.
Babu wata sahihiyar hujjar da ta tabbatar cewa Mutu ya lissafa wannan kadara a cikin kadarorin da ya mallaka, a lokacin ya za zama Ɗan Majalisar Tarayya daga Jihar Delta.
Tun daga neman kamfanin za zai taimake shi ya yi wa kamfani rajista a waje har zuwa kuɗaɗen da ya gabza da kuma cinikin gida da sayar da gidan, duk a asirce ya yi haka.
A takaice dai har yanzu bai lissafa su a cikin kadarorin da ya mallaka ba. Wannan kuma karya dokar Najeriya ce.
Ya kafa Forest Company tun a ranar 27 Ga Okotoba, 2003, watanni shida bayan an sake rantsar da shi karo na biyu. Kamfanin ya na da lambar rajista ta RC 497907.
Kuma shi na cikin daraktocin kamfanin, shi da matar sa Blessing Mutu, Faith Enifome Azeza, Isaac Enifome da Rapheal Ebomo.