Tsohon Gwamna kuma Peter Obi ya maida raddi ga PREMIUM TIMES, bayan an buga labarin yadda riƙa karyar dokokin waske wa biyan haraji ta hanyar haramtacciyar hada-hadar da ya riƙa yi a waje.
Amma maimakon ya tafi kai-tsaye a kan kawo hujjojin da zai kare kan sa, sai ya karkace, ya waske ya na soki-burutsu domin sake bagaras da ‘yan Najeriya.
An buga labarin yadda Peter Obi ya shekara uku ya na gudanar da harƙalla ta ɓarauniyar hanyar da kauce wa dokar hada-hada. Obi ya ci gaba da riƙe muƙamin sa na Darakta, a kamfanin sa da ke Birtaniya, mai suna NEXT International (UK) Limited, har tsawon watanni 14 bayan rantsar da shi Gwamnan Jihar Anambra.
Hakan kuwa da ya aikata ya karya Dokar Sashe na Shida na Dokar Tsarin Aiki ta Najeriya.
Abu na biyu kuma Obi ya yi amfani da wasu dabaru inda ya ɓoye kamfanonin sa da ke ƙasashen waje, waɗanda shi da kan sa ya yarda cewa bai bayyana su a cikin kadarorin sa a lokacin da ya cika fam ɗin takarar gwamna, kamar yadda dokar Najeriya ta tanadar ba.
Yin hakan kuwa ya karya Sashe na 11 Kundi na Biyar na Dokar 1999.
Na uku, yin amfani da Asusun Ƙasashen Waje a matsayin sa na gwamna, haramun ne a dokar Najeriya. Obi ya kasa kare wannan fallasa da aka yi masa.
Borin-kunya:
A cikin raddin da Kakakin Yaɗa Labaran Peter Obi mai suna Valentine Obienyem ya aiko wa PREMIUM TIMES, ya haƙiƙice cewa bai karya dokar Najeriya ko ɗaya ba.
Sai dai kuma ya kasa kare kan sa daga hujjojin da PREMIUM TIMES ta yi amfani ta buga labarin yadda ya karya dokokin.
Maimakon kawo hujjoji, sai Peter Obi ya waske, ya riƙa tado waɗansu batutuwan da PREMIUM TIMES ba ta yi maganar su ba.
“To abin mamaki dai shi ne gaba ɗaya a cikin labarin da PREMIUM TIMES ta buga, babu inda aka ce ya saci kuɗaɗe kafin hawan sa da bayan saukar da gwamnan Anambra.” Haka ya rubuta.
Tabbas rahoton PREMIUM TIMES bai zargi Obi da satar kuɗaɗe ba, kuma ba a gano haka a binciken mu ba.
Yayin da aka tunkari Obi da abin da aka gano a kan sa, bai ƙaryata cewa ya ƙi bayyana kadarorin sa ba. Ya amince bai bayyana ɗin ba.
Kuma bai kare kan sa daga mallakar asusun ajiyar kuɗaɗe ƙasar waje ka na gwamna haramun ne ba.
Haka bai ƙaryata cewa da mu ka buga shi darakta ne a wasu kamfanonin ƙasashen waje ba. Bai ce labarin ƙarya ne ba.
Peter Obi shaida wa PREMIUM TIMES ya yi cewa shi a lokacin bai san ya karya doka ba.
” Ban bayyana kadarorin da na mallaka tare da iyali na ba. Idan ni da iyali na mu na da dukiyar da mu ka yi gamayyar mallaka, ban bayyana ta ga Hukumar CCB ba. Ko ma wata wadda mallaka tare da wani daban.”
Da wakilin PREMIUM TIMES ya nuna masa inda doka ta ce ko shi da wa ya haɗa kasuwanci, sai ya bayyana kadarar, sai ya ce shi a lokacin bai san wannan dokar ba.
Sai dai kuma binciken da PREMIUM TIMES ta bankaɗo, ya nuna cewa Peter Obi shi kaɗai ke da waɗancan kamfanoni na ƙasar waje, waɗanda ya ce na haɗin-gwiwa ne.