Tun bayan da jigon jam’iyyar APC Bola Tinubu ya koma zama a birnin Landan ƴan Najeriya musamman manyan ƴan siyasa ke tururuwa zuwa birnin Landan domin duba shi.
Tinubu na jinyar rashin lafiya ne a birnin Landan, sai dai kuma gidan da yake zaman jinyar a ciki gida ce da ce da aka yi harkallarta, wanda aka siye shi da kudin sata.
Wannan gida sananniyace wanda an yi ta tafka shari’a a kanta kan yadda wanda ke da shi ya malaketa tun a farko.
Kola Aluko shine mai mallakin wannnan gida a birnin Landan da hatta gwamnatin Najeriya sai da ta nemi kotu ta kwace wannan gida saboda an gano cewa da kudin sata aka siya wannan katafaren gida.
Aluko na daga cikin gaggan ƴan harƙallar da ake zargi ya rika taya tsohuwar ministan Man Fetur, Diezani Allison Madueke jibge kuɗaɗen sata a kasashen waje.
A daidai ana shari’ar kwace wannan gida ne daga hannun Aluko, sai kwatsam kaya siyar da gidan.
Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola tare da abokin harkallarsa karkashin wani kamfani suka sayi wannan gida.
Bincike ya bankaɗo cewa wannan gida an saye shi ne da ga hannun Aluko akan Fam miliyan 8, wanda a baya an siya gidan akan Fam miliyan 11 da ƴan kai.
Ba a san dalilin da ya sa Aluko da makarraban sa da suka siyar da gidan kasa da kudin da suka saye shi ba.
Wannan gida ne dai Tinubu ya ke zaune a ciki sannan kuma a wannan gida ne shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai wa Tinubu ziyara a lokacin da ya tafi birnin Landan.
Abin tambaya a nan shine, duk da cewa gwamnatin Buhari ce ta yi kokarin kwace wannan gida saboda harkallar dake cikin ta da kuma kai ruwa rana da aka yi ta yi akan shi a kotun Najeriya da nan kasar, amma kuma shugaba Buhari ya kai ziyara wannan gida.
An bankado cewa shi kansa kamfanin da aka yi amfani da shi wajen siyan gidan kamfani ne da kafa ta saboda kauce wa biyan haraji da kuma yin harkalla irin haka wanda mallakin gwamnan jihar Osun na yanzu ne, Gboyega Oyetola, wanda ya siya wa kansa wannan katafaren gida.
Kamfanin wanda mallakin gwamnan jihar Osun ne Oyetola wanda daga baya ya zare hannun sa daga kamfanin ya naɗa ƴaƴan sa manyan darektocin kamfanin tare da abokin sa da suka kamfanin tare.
Gwamnoni musamman gwamnonin yankin kudu maso yamma sun ziyarci wannan gida domin gaida Tinubu. Yan siyasan jihar Legas da na yankin da wasu daga Abuja duk sun kai gaisuwa wannan gida.
Shima gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje wanda Aminin Tinubu ne shima ba abarshi a baya ba wajen ganawa da Tinubu a wannan gida ba.
Oyetola ya karya dokar Najeriya na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan darektocin Kamfanin Aranda kuma masu mallakin Kamfanin a lokacin da yake shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Osun a lokacin mulkin Rauf Aregbesola.
Dokar Najeriya bai amince wa wanda ke rike da muƙamin gwamnati ba ya ci gaba da zama darekta a wani kamfani ba.
Oyetola bai janye daga kamfanin ba sai gab da zai zama gwamnan jihar Osun.
Ƴan jarida 300 ne dake karkashin kamfanoni aikin jarida 150 a faɗin duniya suka gudanar da wannan bincike na Pandora papers.
A Najeriya, jaridar PREMIUM TIMES ce kawai jaridar da ta yi aiki tare da sauran kamfanoni na duniya wajen bankaɗo harkallar da attajirai da masu faɗa aji a kasashen duniya suka tattafka ta hanyar amfanibda haramtattun kamfanoni donnkauce wa biyan haraji da kuma tara kazamin dukiya.
Discussion about this post