A ci gaba da fallasa da bankaɗe-bankaɗen karkatar da kuɗaɗe, Pandora Papers sun bankaɗo wata gadangarƙamar alaƙar da aka ƙulla tsakanin tsohon Mashawarcin Goodluck Jonathan da Shugaba Muhammadu Buhari a Fannin Tsaro, Sambo Dasuƙi, shi da ƙasurgumin biloniyan da aka ba kwangilar aikin gina tashar samar da hasken lantarki ta Mambilla.
Alaƙar a tsakanin su dai ta ƙullu ne a lokacin da sai yadda Dasuƙi ya ga dama ya ke damawa, a watanni 37 da ya yi ya na kan muƙamin mashawarci kan harkokin tsaro.
Leno Adesanya: Ɗan Kwangilar Da Ya Iya Jan Zaren Tsula Tsiya:
Cikin shekarar 2013 ce gawurtaccen ɗan kwangila Leno Adesanya ya tuntuɓi ya tuntuɓi wani kamfani da ke Tsibirin British Virgin Islands (BVI), mai suna Trident Trust Company Ltd, domin ya yi kurɗa-kurɗar yin rajista ga wani kamfani da iyalan Sambo Dasuƙi za su kafa. Sunan kamfanin Hydropower Investments Limited.
An yi wa kamfanin rajista bisa cewa zai riƙa harkokin zuba jari da kuma sayen kadarori.
A cikin yarjejeniyar kafa kamfanin, an rattaba cewa Hydropower Investments Limited zai mallaki hannayen jari miliyan 1.5 a cikin wani kamfani mallakar Adesanya da wani mai suna Uche Nwokedi. Sunan kamfanin Sino Africa (Nigeria) Limited.
Haka kuma Hydropower Investments Limited zai mallaki hannayen jari miliyan 10 a cikin kamfanin Sunrise Power & Transmission (Nigeria) Co. Limited.
Shi kuma Sunrise Power & Transmission Co., shi ne aka fara bai wa kwangilar aikin gina tashar wutar lantarki a Mambilla.
Kuma shi ne dai har yanzu ake ta tafka ƙadabolon rikici da shi a kan kwangilar, rikicin da ya hana mashahurin bankin nan na Chana, Chinese Exim Bank zuba kuɗaɗe, domin a fara aikin ginin tashar wutar a Mambilla.
An yi wa kamfanin iyalan Dasuƙi rajista a ranar 13 Ga Nuwamba, 2013. A cikin Daraktocin kamfani akwai Leno Adesanya, wani ɗan Sambo Dasuƙi mai suna Abubakar Atiku Dasuƙi.
Adesanya ba shi da hannun jari a cikin kamfanin, amma kuma sunan lambar gidan sa na Legas ne adireshin kamfanin.
Waɗanda ke da hannayen jari a cikin kamfanin na Hydropower Investments & Transmission Co. Limited, akwai Abubakar Atiku Dasuƙi, mai hannayen jari 17,000. Sai Hassan Dssuƙi mai hannayen jari 16,000. Ana kuma kiran Hassan da suna Sultan. Ita kuma Asma’u Iman Dssuƙi ta na da hannayen jari 16,500 a cikin kamfanin.
Dukkan su ukun ‘ya’yan Sambo Dasuƙi ne, kuma an kafa kamfanin a lokacin da Dasuƙi ke mashawarcin harkokin tsaro ga Jonathan.
Babu wata hujja da ta nuna cewa Dasuƙi ya kwashi kuɗi ya zuba a kamfanin. Amma duk lokacin da aka nemi Adesanya ya bayar da cikakken bayanin masu kamfanin, sai ya ce wa mahukunta a ƙasar waje cewa kamfanin na wani ɗan uwan sa ne, kuma ba shi da gidan kan sa, a gidan shi Adesanya ɗin ya ke a raɓe.
Sannan kuma ya riƙa ce masu bashi ne za a karɓo a zuba cikin kamfanin a matsayin kuɗaɗen da zai fara aiki gadan-gadan, kuma shi Adesanya ne zai samo bashin.
Adesanya ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa Dasuƙi bai yi masa wata alfarma ba. Kawai shi dai ya taimaka wa ‘ya’yan Dasuƙi ɗin ne sun kafa kamfani, domin su samu tsayawa da ƙafafun su.
Shi ma Dasuƙi ya yi magana da PREMIUM TIMES ta bakin wani wakilin sa. Ya ce babu ruwan sa a cikin batun kafa kamfanin. Domin bai ma san Adesanya ya kafa kamfanin da sunan ‘ya’yan sa ba.
Sannan kuma ya ce ai ‘ya’yan sa sun girma, sun kai munzilin iya kafa kamfanin da za su yi harkokin su.
Sai dai kuma a nan Najeriya Adesanya ne kaɗai aka sani a matsayin mai kamfanin. Ya hana mahukunta su san akwai sunan iyalan Sambo Dasuƙi a ciki. Kuma shekaru takwas kenan babu batun sauya wa kamfanin suna a Hukumar Rajistar Kamfanoni ta Kasa (CAC).
A lokacin da Adesanya ya samu matsala da Gwamnati dangane da kwangila a NNPC, ya kusanci Dasuƙi an riƙa shiga ana fita.
Sai dai kuma a ƙarshe ya kai ƙara kotun sasanci ta Paris Court of Appeal, kuma ya yi nasara.
Duk da a lokacin mulkin Jonathan an biya Adesanya tsabar kuɗi dala miliyan 55.3 kuɗin kashe rigima, har yau tsugune ba ta ƙare ba.
Sai kuma rikicin aikin kwangilar gina tashar wutar Mambilla da aka bai wa kamfanin Adesanya, wato Sunrise Powers and Transmission Company Ltd, ta dala miliyan 6. A yanzu wannan kwangila ta zame wa gwamnati da ‘yan Najeriya alaƙaƙai.
Discussion about this post