Shekaru 11 da su ka gabata, a lokacin da Gwamnan Jihar Kebbi na yanzu, Abubakar Bagudu ke Sanata, ya tura wata tawagar ‘yan ƙaƙudubar sa zuwa ƙasar Singapore. Ya tura su ne domin su samo masa wurin da zai ɓoye wasu ƙazaman biliyoyin kuɗaɗe.
Waɗannan kuɗaɗe dai a yanzu haka su ne ake tafka kwatagwangwamar shari’a a Amurka, sakamakon bankaɗo kuɗaɗen da aka yi, kuma mahukuntan Amurka ke ƙoƙarin ƙwace su daga hannun Bagudu.
Masu bincike sun gano cewa kuɗaɗen da Bagudu ya ɓoye su na cikin biliyoyin dalolin da ya taimaki iyalan marigayi Shugaba Janar Sani Abacha su ka ɓoye bayan sace su daga Najeriya, a cikin shekarun 1990s.
Bagudu ya samu wani kamfani mai suna Asiaciti Trust, domin ya ɗauki gaban-gabarar aikin ɓoye masa ƙazaman kuɗaɗen a Singapore.
Shi dama Asiaciti Trust, wanda babban kamfanin lauyoyi ne, ya shahara wajen lauyar wa ɓarayin gwamnati ƙazaman kuɗaɗen da su ka sato daga ƙasar su zuwa wata ƙasa.
Domin ko a baya-bayan nan cikin Yuli 2020, sai da Hukumar Sa-ido Kan Hada-hadar Kuɗaɗe a Singapore ta ci Asiaciti Trust tarar dala miliyan 1.1 saboda wani laifin karya doka. Sun aikata laifin tun a cikin 2007 da 2008.
Gungun ‘Yan Ta-kifen Kifar Da Talakawa:
A ranar 23 Ga Fabrairu, 2010, tawagar Bagudu wadda ta ƙunshi ƙanin sa Ibrahim Bagudu da wani tantirin lauya ɗan Landan, mai suna Ben Davies na Ofishin Lauyoyin Byrne & Partners sun haɗu da jami’an ƙaƙudubar Asiaciti Trust su ka yi wa dukiyar Atiku Bagudu rajistar sirrin yadda za a riƙa ɓoye ta asiri rufe.
An ɗora wa Asiaciti Trust aikin karkatar da ƙaramar dukiyar da Atiku Bagudu ya ɓoye a cikin 1997 a wani kamfanin sa mai suna Ridley Trust and Ridley zuwa cikin Asiaciti Trust daga Tsibirin Virgin Islands zuwa Singapore.
Bayan ‘yan watanni an gabji dala miliyan 99 daga Ridley an gabza a Asiaciti Trust.
An dai san Atiku Bagudu a matsayin yaron iyalan da ke masu harƙallar ɓoye kuɗaɗen sata a ƙasashen waje. Ba a san yadda aka yi shi ma ya narke ya zama gogaggen jan-wuyan da ya riƙa ɓoye na sa kuɗaɗen da ya riƙa gabza a harƙallar sata-ta-saci sata ba.
Pandora Papers gamayyar ƙungiyar wasu mashahuran ‘yan jarida ne na duniya da kungiyoyin fafutikar yaƙi da rashawa sama da 150. Akwai wasu ‘yan PREMIUM TIMES a cikin kungiyar.
Su ne ke aikin bankaɗo harƙallar da manyan ‘yan siyasa masu ci da na baya da sauran shugabanni su ka danne.
Asiaciti Trust sun taimaka wa Atiku Bagudu ya kafa kamfanonin ɓoye ƙazaman kuɗaɗen sata a ƙasashe uku da su ka haɗa da Singapore, Cook Islands da Birtaniya.
An rubuta sunayen Atiku Bagudu, matar sa, ‘ya’yan sa bakwai da ɗan’uwan sa Ibrahim a matsayin masu haƙƙi kan dukiyar.
A cikin 1988 Abacha ya mutu, kuma zuwa 2020 an dawo da dala biliyan 3.6 na ƙananan kuɗaɗen da su ka sata, su da babban gogarman ɗan-fiton su Atiku Bagudu, wanda a yanzu shi ne Gwamnan Jihar Kebbi.
Tsare Atiku Bagudu A Kurkukun Amurka:
Cikin 2003 an bankaɗo dala miliyan 163 a hannun Bagudu a Jersey, har aka tsare shi watanni shida. Ya cimma yarjejeniya da masu gabatar da ƙara aka maido kuɗaɗen Najeriya, shi kuma ya nemi kada a maida shi Najeriya, tunda ya biya kuɗaɗen.
PREMIUM TIMES HAUSA ta taɓa buga labarin ɗaure Bagudu a kurkukun Amurka, saboda mahukuntan ƙasar sun gano ƙasurgumin ɓarawon kuɗaɗen gwamnatin Najeriya ne.
Sannan kuma dala miliyan 308 da aka bankaɗo cikin 2020, su ma Atiku Bagudu ne ya karkatar da su.
Atiku ya yi tsamo-tsamo cikin harƙallar karkatar da ƙananan biliyoyin dalolin satar Abacha a bankunan ƙasashen Virgin Islands, Ingila, Guensey da Jersey.
BA GUDU BA TSORON DANNE HAƘƘI:
Wannan gagarimin labari ne a kan yadda manyan ɓerayen Najeriya ke satar maƙudan kuɗaɗe, su na jibgewa ƙasashen waje, a lokacin da talakawan ƙasa ke sharar ɓarci bayan sun gama gaganiyar neman abincin magance yunwar rana ɗaya wadda su ka tsinci kan su bayan masu sace kuɗaɗen kuɗin ƙasa sun jefa su cikin kwazazzabon ƙuncin rayuwa.