Zargi: Wani bidiyo da ake yadawa a manhajar WhatsApp, dake nuna hotunan wasu gawarwaki babbake kurmus wai wasu Fulani ne ‘kwarankwatsa tannatsa’ ya hallaka su a daidai sun dunguma da makamansu za su kai wa wasu kiristoci a yankin Arewacin Najeriya hari, kafin su kai tsawa ya halaka su, ba gaskiya bane.
Kwanan na wani bidiyo mai tsawon dakiku 29 wanda aka yi ta yaɗa wa a manhajar WhatsApp ya yi zargin cewa Fulani ‘yan bindiga ne kwarankwatsa tannatsa’ daga sararin samaniya ya faɗo a kansu ya babbake su duka wai a hanyarsu su na kai hari ga wasu al’ummar kiristoci da ke yankin Arewacin Najeriya.
Bidiyon ya nuna hotunan gawawwaki da dama da barabuzan kayayyaki da baburan da suka kone. Akwai kuma muryoyin da ke magana a wani harshen da ba za’a iya tantancewa ba, da wuta r gobara, da kuma wasu mutane masu kama da ma’aikata.
Bidiyon wanda ya yi kama da wani wajen da tankar mai ta fashe na dauke da kalaman da ke cewa “gawarwakin Fulani ‘yan bindiga bayan da tsawa daga sama ya fado a kansu duka ya babbake su yayin da su ke hanyar zuwa kai hari wata al’ummar kiristoci a Arewa. Wannan ya nuna lallai Allah na amsa addu’o’in Kiristoci. Hotunan na da tayar da hankali.
Tantancewa
Da farko dai mun gano cewa an taba amfani da wannan bidiyon domin nuna dakarun Najeriya suna kai hari kan ‘yan bindiga a jihar Zamfara wanda Dubawa ta riga ta karyata.
Dan haka ne mai binciken wannan labari ya daukar wannaa bidiyo domin sake yi masa binciken kwakwaf ta hanyar amfani da manhajoji binciken kwakwaf na zamani da suka haɗa Tineye da INVID ba tare da samun nasara cewa wani sabon bidiyo da ban da wanda aka taɓa amfani da shi a baya
Da muka yi amfani da manhanjan Yandex sai muka gano cewa tun shekarar 2019 ake soma amfani da bidiyon domin ya bayyana a shafuka da dama a ciki har da Facebook. Daya daga cikin su ma wani ma’aikacin Random FB ne ranar 5 ga watan Satumba 2019 wanda aka yi wa taken. “Wannan tsokanan zai iya janyo yaki …. A Afirka ta kudu.
Wani labarin da aka wallafa a norskk square space ranar 18 ga wata Satumba 2021 mai taken “Afirka ta Kudu, kasar da ta gaza” na zargin cewa fada da kashe-kashe ba wani sabon abu ba ne a tsakanin mutanen Africa kuma ko shi ma wasu daga cikin hotunan bidiyon daga nan aka dauko su. Toh Kaji!!
Da muka duba kalmomi mun ga cewa a 2019 aka fara daukar bidiyon lokacin da wata tanka ta fashe ta yi sanadiyyar rayuka 60 ta kuma jikkata da dama a kasar Tanzania. Tankar na hanyar zuwa Dar es Salaam ne, wadda itace birni mafi girma kafin ta kife a garin Morogoro bisa bayanan da gidan talbijin na Aljazeera ya wallafa.
Rahoton ya bayyana cewa bayan motar ta faɗi mazauna garin sai suka yi tururuwa zuwa wannan wuri domin ɗibar ganimar man dake ta kwarara, a wannan lokaci ne motar ta yi bindiga ta babbake mutanen sama da 60.
A Karshe
Tantancewar da Dubawa ta yi ya nuna cewa wannan bidiyo dai an ɗauke shi ne a shekarar 2019 a kasar Tanzania a lokacin da wata tankar mai ta faɗi, mutanen gari kuma suka yi tururu zuwa wurin domin ɗibar ganimar mai dake kwarara, daga nan ne motar ta yi bindiga gobara ya tashe. Mutum sama da 60 suka babbake, amma ba wai ,’kwarankwatsa tannatsa’ bane ya lashe wasu Fulani duk suka babbake a hanyar zuwa kaiwa Kiristoci hari a Arewacin Najeriya.