Sunan tsohon shugaban ƙungiyar ƴan jaridu ta ƙasa NUJ kuma tsohon shugaban ƴan jaridu na nahiyar Afirka kuma kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Malam Muhammad Garba ba baƙon suna bane musamman idan aka yi la’akari da yadda ya samu gogewa tare da ƙwarewa a harkar aikin jarida a ciki da wajen jihar Kano.
Haka kuma kamar yadda tarihin wannan gogaggen ɗan jarida ya nuna cewa ya fara aikin jarida ne tun daga shekarar 1989 a kamfanin buga jaridu na Triumph wanda ya ke mallakin jihar Kano ne. A cikin irin aikace-aikacen da ya yi a harkar yaɗa labarai da aikin jarida ya taɓa yin sakataren yaɗa labarai na mataimakin shugaban majalisar wakilan Najeriya a cikin shekarar 1993.
Amma duk da tarin ilimi da ƙwarewa da sanin aiki da Malam Muhammad Garba ya ke da shi sai ga shi a farko makon nan da mu ke ciki al’ummar Najeriya su ka cika da mamaki tare da al’ajabin yadda wannan ɗan jarida ya yi wani abu da za a ce abin kunya ko kuma makuwa ce a aikin jarida, domin idan da a ƙasashen da su ka cigaba ne babu shakka da tuni Muhammad Garba ya daɗe da sauka daga kan wannan muƙami saboda wannan abin kunya da ya tafka.
Duk da cewa masana da masu sharhi akan al’amuran yau da kullum sun daɗe suna batun cewa duk ɗan jaridar da ya karɓi aiki a gurin gwamnati irin ta siyasa to babu shakka ya zama ɗan amshin shata ma’ana sai abin da mahukunta su ke so zai faɗa akan kowacce irin mas’ala kuma ko da hakan zai zubar masa da martaba da darajar aikin da ya shekara yana nemawa kan sa.
Amma kuma a ɗaya ɓangaren kowa yana sane da cewa tsira da martaba da mutunci ya fi duk wani abu da bawa zai samu a wannan sararin duniyar. Haka kuma ga mutane irin su Muhammad Garba da su ka shafe fiye da shekaru 30 suna fafatukar gina rayuwar aikinsu akan daraja da martaba da kuma ƙima, abin mamaki ne ƙwarai da gaske a ce rana tsaka su ɓarar da wannan gini na tsahon shekaru.
Menene Ya Faru?
A ranar Litinin 5 ga watan Oktoban nan da mu ke ciki jaridar Premium Times da ke shafukan intanet ta rawaito cewa hukumar EFCC da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta kama Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje wacce ita ce uwargidan gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, kan tuhuwar rashawa da zambar fili da ɗanta ya kai kararta.
Baya ga jaridar ta Premium Times kafafen yaɗa labarai irin su Daily Trust da BBC Hausa da DW da Rfi da VOA duk sun rawaito wannan labarin. Kuma babu shakka shi kan san Malam Muhammad Garba ya yi imani da cewa babu yadda za a yi waɗannan kafafen yaɗa labarai na gida da na waje da duniya ta aminta da sahihanci da ingancin labaransu su haɗu akan labari guda wanda kuma ba sahihi ba ne! Abu ne mai wahala.
Domin wata tabbatacciyar majiya daga fadar gwamnatin Kano da ta buƙaci a sakaye sunanta ta sanarwar da sashen Hausa na BBC cewa jami’an hukumar EFCC ne suka je har Kano suka kuma tafi da Hafsat Abdullahi Umar Ganduje kamar yadda ake kiran ta, zuwa Abuja, dominn amsa tambayoyi masu nasaba da korafin da danta ya gabatarwa da hukumar.
Sai dai jim kaɗan da bullar wannan labari sai ga shi Malam Muhammad Garba ya fitar da wata sanarwar da ke ikirarin cewa wannan labari ƙarya ne ma’ana ba shi da tushe balle makama! Kaico!
Amma a wani al’amari mai kama da tufka da warwara tare da rashin ƙwarewar wasu daga cikin masu taimakawa gwamnatin Kano akan harkar yaɗa labarai sai ga shi ɗaya daga cikin masu taimakawa Gwamna Ganduje kan yaɗa labarai ya wallafa wasu hotuna a shafukan Facebook da ke nuna Hajiya Hafsat Abdullahi Umar Ganduje tana sauka daga jirgin sama a filin tashi da sauka na Malam Aminu Kano da ke birnin Kano.
Wannan jami’i ya ƙarawa hoton da wani gajeren rubutu kamar haka “Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR, tare da mai ɗakinsa Prof. Hafsat Abdullahi Umar Ganduje sun sauka a filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano bayan dawowa daga birnin Tarayya Abuja a safiyar wannan rana. Yau, Talata 5/10/2021”
Abin lura a nan shi ne ko iya wannan kaɗai ya isa a ce Malam Muhammad Garba ya ƙi amincewa ya fitar da sanarwar da ke nuna cewa labarin gayyatar da hukumar EFCC ta yiwa uwargidan Gwamnan Kano ƙarya ne. Domin hotunan sun jefa kokwanto tare da shakku kan al’amuran biyu, wato batun kwamishinan cewa “Goggon” ba ta je Abuja ba da kuma hotunan da ke nuna dawowar ta Kano.
Hakazalika, idan har irin waɗancan kafafen yaɗa labarai za su rawaito labarin da su ke da ingantacciyar madogara tare da hujjoji ƙwarara, amma kawai dan ya saɓawa wani mai mulki sai kawai a fito a ce labarin ƙarya ne to waɗanne kafafen yaɗa labarai ne ke nan za su rawaito sahihin labari?
Yanzu dai tambayar guda ɗaya ce: Shin tsakanin Premium Times da Daily Trust da BBC da DW da Rfi da VOA da kuma Malam Muhammad Garba wanene mai gaskiya da ƴan Najeriya za su yarda da shi?
Al’umma su ne Alƙalai!
Buhari Abba ɗan jarida ne ya rubuto daga Kano – Najeriya. buhariabba57@gmail.com