Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa tarihi daban-daban, wanda talakawan da su ka zaɓe shi ba za su taɓa mantawa da shi ba.
A zamanin sa kayan abinci sun yi tsadar da ba su taɓa yi a baya ba. Man fetur ya yi tsadar da bai taɓa yi a baya ba. Rayuwa ta yi ƙuncin da a baya ba ta taɓa yi ba. Talakawan yankin Arewa wato Mazaɓar da Buhari ya fito, ba su taɓa shiga bala’in ‘yan bindiga ba kamar zamanin Buhari, musamman har da jihar sa ta haihuwa, Katsina.
Duk tsawon wannan ƙunci da bala’in da ƙasar nan ke ciki, wani abin da Shugaba Buhari ya fi maida hankali a kai, shi ne ciwo bashi.
Ƙididdiga ta nuna bashin da Buhari ya ciwo a ƙasashen waje ya nunka wanda ya gada a hannun gwamnantoci uku da daka yi kafin shi daga 1999 zuwa 2015 kafin ya hau mulki.
Obasanjo: Ya Gaji Bashin Dala Biliyan 28 A 1999:
Sojoji sun bar Najeriya cikin ɗimbin bashin Dala Biliyan 28 bayan sun sauka a 1999, sun miƙa mulki a hannun farar hula, ƙarƙashin shugaban da aka zaɓa a lokacin, Olusegun Obasanjo.
Yayin da Obasanjo ya hau, ya maida hankali wajen ganin ƙasashe da cibiyoyin bayar da lamuni da ke ƙarƙashin ‘London Club’ da ‘Paris Club’ sun yafe wa Najeriya basussukan da su ke bin ta.
Lokacin da Obasanjo ya sauka a 2007, ya bar bashin Dala Biliyan 2.11 kaɗai a kan Najeriya.
Yar’Adua: Daga lokacin da marigayi Shugaba Umaru ‘Yar’Adua ya hau mulki zuwa rasuwar sa, har zuwa sauran zangon farko da Jonathan ya ƙarasa masa, Dala Biliyan 1.39 kaɗai aka ƙara ciwowa bashi.
Jonathan: Goodluck Jonathan ya ramto Dala Biliyan 3.8 kaɗai a zamanin mulkin sa. Idan an haɗa na Obasanjo da Yar’Adua da na Jonathan ɗin, kenan Buhari ya gaji bashin Dala Biliyan 7.3.
Buhari: Daga 2015 Zuwa 2020: Buhari ya kinkimo bashin Dala Biliyan 21.27.
Wato idan an haɗa da wanda ya gada, yanzu ana bin Najeriya bashin Dala Biliyan 28.57 kenan.
Kada a manta, Buhari na ƙoƙarin ciwo wani bashi na sama da Naira Tiriliyan 2 a waje. Kuma akwai wanda ya ke neman amincewar Majalisar Dattawa ya ciwo na Naira Tiriliyan sama da 5.
Tulin Bashin Da Ake Bin Najeriya A Cikin Gida:
Sojoji sun bar wa Obasanjo dagon bashin Naira Biliyan 795.
Zuwa 2015 ranar da Buhari ya hau mulki, a nan cikin Najeriya ana bin ƙasar bashin Naira Tiriliyan 8.8.
Buhari ya hau mulki a 2015, amma kuɗin da ake bi bashi a cikin gida sun nunka zuwa Naira Tiriliyan 16.2 a daidai ƙarshen 2020.