Wani rahoto da aka fitar a ranar Talata ya bayyana cewa idan ba a yi gaggawar ɗaukar matakan da su ka dace ba, to nan da shekarar 2030 aƙalla marasa galihu 118 za su za rasa tudun dafawa a Afrika, sanadiyyar ƙarancin ruwan sama, ambaliyar ruwan sama da kuma tsananin zafi a sassa daban-daban na nahiyar Afrika.
Rahoton wanda Ƙungiyar Kula da Yanayi ta Duniya (WMO) ta fitar tare da haɗin guiwar Ƙungiyar Bunƙasa Tattalin Arzikin Afrika, sun nuna cewa zaizayar ƙasa da fari da ambaliya da kuma tsananin zafi na yi wa ƙasashen Afrika barazana matuƙa.
Rahoton ya ce waɗanda wannan gagarimar matsala za ta shafa, akasari duk masara galihu ne, waɗanda samun su na rana ɗaya bai kai dala 1.9 ba.
Haka kuma rahoton ya ce wannan matsala idan ta ƙara maƙasura, za ta haifar da raguwar ƙarfin tattalin arzikin ƙasashen Afrika da kashi 3 bisa 100.
Zaizayewar Tsibirai A Afrika:
Wata babbar barazana da rahoton ya ce na fuskantar Afrika, ita ce zaizayewar manyan tsibiran Afrika guda uku.
Rahoton ya tabbatar da cewa tsibiran su na zaizayewa. Daga 1880 zuwa yau sun ragu da kashi 20 bisa 100 na girman su.
Waɗannan tsibirai sun haɗa da Tsibirin Masif na Kenya, Tsibirin Rwenzezi sai kuma Tsibirin Kilimanjaro da ke Tanzania.
Sama da ƙasashen Afrika 20 ne su ka fuskanci ambaliya a 2020, ciki har da Najeriya.
Ana Wata Ga Wata: Fatara da Yunwa Sun danne Mutum Miliyan 120 Cikin 2020, Cewar UN:
Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Gutteres ya bayyana cewa akwai alhaki da rashin tausayi ga masu hali, ganin yadda miliyoyin mutane ke ƙara faɗawa cikin yunwa da fatara da talauci a duniya.
Da ya ke bayani a a Ranar Jimamin Yaƙi da Fatara da Yunwa a Duniya, wato ranar 17 Ga October, Gutteres ya ce abin takaici ne a ce a cikin shekarar 2020 mutum fiye da miliyan 120 sun afka cikin ƙuncin fatara, yunwa da talauci a duniya.
Ya nuna damuwa dangane da yadda ake ƙara samun rata da tazara mai yawa tsakanin masu hali da faƙirai da matalauta.
” A yayin da mu ke yaƙin ganin an kawar da yunwa a duniya, to kuma wajibin mu ne mu ga an rage rata da tazarar da ke tsakanin masu hali da matalauta.
” Annobar korona ta jefa aƙalla mutum miliyan 120 cikin ƙuncin rayuwa a duniya. Haka nan kuma yadda ake samun fifikon wadatar rigakafin korona a wasu nahiyar fiye da wata nahiyar, shi ma ya ƙara bazuwar cutar a inda babu wadatar makarai da riga-kafi sosai.
” Ko kafin ɓarkewar cutar korona, dukiyar manyan attajiran duniya su 22, ta zarce yawan dukiyar da matan Afrika arankatakaf su ka mallaka.”
Gutteres ya ce idan mutum ya ƙara da cewa rata da tazarar da ke tsakanin mai hali da faƙiri sai ƙara faɗaɗa ta ke yi.
Ya jaddada ƙudirin Hukumar UNDP na fitar da mutum miliyan 100 daga cikin fatara da yunwa tsakanin 2022 zuwa 2025.