Yayin da ake kukan cewa cutar korona ta haifar da ƙuncin rayuwa da karantar tattalin arziki, a gefe ɗaya kuma Bankin Duniya (World Bank) ya amince a a bai wa Najeriya lamunin dala miliyan 400, domin sayen riga-kafin allurar korona.
A ranar Juma’a ce Bankin Duniya ya sanar cewa Daraktocin bankin sun amince a ƙara ɗirka wa Najeriya bashin, baya ga wanda aka bai wa ƙasar a ƙungiyar IDA ta Bankin Duniya.
Yayin da Bankin Duniya ya fitar da sanarwar a birnin Washington na Amurka, ya ce an amince za a bayar da kuɗaɗen ne domin a yi aikin samar da rigakafin korona da kuma gagarimin aikin yi wa ‘yan Najeriya rigakafin mai inganci, kuma a cikin nasara.
Wannan shiri dai ana buƙatar yi wa aƙalla ‘yan Najeriya miliyan 40 rigakafin korona kuma ganin an tallafa wajen ganin aƙalla mutum miliyan 110 sun samu dama ko sauƙin yin rigakafin.
Daga cikin bashin har yau za a yi amfani da wasu kuɗaɗen domin yi shiri da kimtsin bijiro da hanyoyin kaucewa ko shawo kan duk wata barazana da za ta iya fuskantar fannin kiwon lafiya nan gaba.
“Wannan lamuni zai bai wa Najeriya hoɓɓasar ganin aƙalla an yi da kuɗaɗen an wajen yi wa kashi 50 bisa 100 na ‘yan Najeriya rigakafin korona, nan da shekaru biyu.”
Daraktan Bankin Duniya mai Kula da Najeriya, Shulbham Chsudhuri, ya ce yayin da Najeriya ke ta ƙoƙarin daƙile korona zango ta uku, to kuma akwai matuƙar buƙatar an ƙara yi wa jama’a da dama rigakafin korona a faɗin ƙasar.
Discussion about this post