Hukumar EFCC ta bayyana cewa danganta farmakin da wasu jami’an tsaro su ka kai gidan Mai Shari’a Mary Odili ta Kotun Ƙoli, ƙarya ce don kawai a kawo saɓani tsakanin ɓangaren Shari’a da EFCC.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labaran EFCC, Wilson Awujeran ya fitar ga manema labarai a ranar Juma’a da dare, kuma ya turo wa Premium Times, ya ce jami’an EFCC ba su kai farmakin ƙoƙarin yin bincike gidan Mary Odili ba.
Jiya Juma’a da dare ne dai jami’an tsaro su ka kewaye gidan Mary Odili, amma jami’an tsaron gidan ta su ka ce ba za su shiga ba, sai da sammacin kotu.
Mary Odili dai ita ce matar tsohon gwamnan jihar Delta Peter Odili, wanda ya shafe shekaru da dama ya na kulli-kurciya da EFCC. Tun bayan saukar da gwamna cikin 2007 ya ke garzayawa kotu ana ba shi kariyar hana EFCC su bincike shi ballantana a gurfanar da shi.
Wasu rahotanni sun nuna cewa Mary Odili ta shaida wa jami’an tsaron cewa ba za ta bari su shiga gidan ta ba, saboda ba gidan mijin ta Peter Odili ba ne, gidan ta ne.
Kakakin SSS Peter Afunanya, ya shaida wa Premium Times ta saƙon tes cewa, “ba SSS ne su ka dira gidan ba.”
Amma wata majiya a Kotun Ƙoli ta jajirce wa Premium Times cewa lallai SSS ne su ka kai farmakin.