Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara ta tabbatar da labarin yadda ‘yan bindiga su ka tare hanya, su ka kwashi ‘yan bautar ƙasa a Jihar Zamfara.
Lamarin ya faru a ranar Juma’a, yayin da su ke kan hanyar su ta zuwa Sansanin NYSC na Jihar Zamfara da ke garin Tsafe.
Majiya ta tabbatar wa wakilin mu cewa an nemi wasu ‘yan bautar ƙasar shida ba a gani ba. Amma dai jami’an tsaro sun ce guda biyu aka yi garkuwa da su.
Rahotannin wasu jaridu ba PREMIUM TIMES ba, ya nuna ‘yan NYSC ɗin sun fito ne daga Jihar Benuwai, kuma akwai mace a cikin waɗanda aka nausa cikin dajin da su.
Majiyar ta ƙara shaida cewa an tare su tsakanin Sheme da ke Jihar Katsina, a Ƙaramar Hukumar Faskari da kuma Tsafe, garin da hedikwatar NYSC ta jihar Zamfara ta ke.
Tuni dai Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Zamfara Ayuba Elkana ya ziyarci sansanin ‘yan bautar ƙasar, inda ya kwantar masu da hankali cewa jami’an sa za su tsare lafiyar su.
Haka kuma ya ce jami’an sa sun bazama cikin daji domin ceto ‘yan uwan na su.
Sansanin wanda ya fara cika da sabbin zuwa daga jihohi daban-daban, ya shiga cikin ruɗani da fargaba, biyo bayan jin labarin garkuwar da aka yi da ‘yan bautar ƙasar tun kafin su isa sansanin da aka tura su.