Bangaren tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau, sun zaɓi Ahmadu Zago a matsayin shugaban jamiyyar APC a jihar a zaɓen shugabannin jam’iyyar da ak gudanar a Kano ranar Asabar
Duk da cewa jami’an tsaro sun hana ɓangaren Shekarau gudanar da zaɓen bayan ƴaƴan jam’iyya sun taru a wajen zaɓe, sun yi zaɓen a Janguza da ke ƙaramar hukumar Tofa dafa baya ranar Asabar.
A ɓangaren gwamna Ganduje ƴan APC sun zaɓi Ɗan sarki Abdullahi Abbas a matsayin shugaban jam’iyyar a Kano.
Duka shugabannin biyu sun rattaba hannun a takardar amincewa su shugabanci jam’iyyar.
Yanzu dai APCn Kano ta daɗa dagulewa domin karshenta kuto za ta raba gaddama tsakanin bangarorin biyu.
Sai dai kuma wanda jam’iyyar APC ta tura Kano ya kula da yadda a ka yi zaɓen, Farfesa Mohammed Bello ya ce an gudanar da zaɓe lafiya, kuma shugaban da ɓangaren sanata Shekarau suka zaɓa ne sabon shugaba APC.
A na su ɓangaren, gwamna Ganduje ya ce duk wani zaɓen da aka yi na shugaban jam’iyya idan ba na ɓangaren sa ba ne wahalar banza aka yi.