Fitaccen mawakin Buhari da APC Dauda Kahutu da ake kira Rarara bayyana cewa gaskiyar Buhari ce ya sa yake yi masa waka ba don kudi ba.
Rarara ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi ta musamman da BBC, inda yake cewa tun yana yaro ake nusantar da shi kan gaskiya da amanar Buhari kuma har yanzu da ya taso ya ga hakan.
A hira da rarara yayi na minti 7 da jaridar, ya ce an yi mishi tayin sama da naira miliyan 500 domin ya daina yi wa Buhari waka amma ya ki.
“An taba ba ni naira miliyan 500 domin na daina yi wa Buhari waka amma na ki karba, saboda duk abin da nake yi ina yi ne domin kasata”.
Ya ce an sha ba shi kudi domin ya hakura da tafiyar Buhari amma a cewarsa bai taba sa shi jin ya yi gezau ba.
“Babban burina na ga ƙasata ta gyaru kamar yadda sauran kasashen duniya suke, kama daga ci gabanta da habbakarta, yaranmu idan sun zo su rika yin alfahari da ita, in ji mawakin.
Ko da yake a yanzu ya ce yana dab da sakin wasu wakoki da za su bayyana irin ayyukan da Shugaba Buhari yake yi da wadanda ya kammala, wanda a cewarsa “mutane za su gamsu da ceton Najeriya da Buhari ke yunkurin yi.”
Mawakin ya ce ya yi wa Buhari waƙa 66, sannan akwai wadanda za su fito nan ba da dadewa ba.
“Yawancin wakokin da nake yi wa Buhari suna zuwa ne daidai da lokaci, ba wai zama nake na rubuta waka akan shi ba.
“Misali ai na yi wakar Masu gudu su gudu na yi ta lokacin da Buhari ya ci mulki, a lokacin ana maganar idan PDP ta ci mulki sai dai mu gudu mu bar Najeriya.
“To Buhari ya ci mulki muma sai muka mayar da marta ni, a wakar, muka ce in kasan ka yi sata ka gudu.
Rarara ya ce a haka aka yi wakar ‘Ga Buhari ya dawo’lokacin Shugaban kasa ya yi rashin lafiya ya je Landan sai aka yi sa a ya ji sauki zai dawo, to a wannan lokacin cikin dare aka yi waƙar da aka ce washegari zai dawo, gaskiya ba na rubuta wakokin Buhari.”
Bayan haka mawakin ya ce a ra’ayin sa, talakawar Najeriya su kara wa Buhari wa’adin shekara 4 zuwa 5 bayan wa’adin sa a 2023 ya ci gaba don ya karisa ayyukan da ya somo.