Kwayar cutar Maleriya da ake haddasa Zazzabin wanda cizon sauro ne ke dasa cutara a jikin mutun gamu da ajalinta yanzu tun kafin ta kai ga illata mutum ta hanyar baje kolinta a cikin jinin mutum tun kafin ta kaishi ga sai ya ga likita.
Bincike ya nuna cewa akalla mutane kusan rabin miliyan da kuma yara daban sama da 260,000 ake rasawa sanadiyyar fama da zazzabin cizon sauro wato maleriya a wannan yankin na Afrika.
Idan ba a manta ba a ranar Laraba ne kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa masana kimiyyar hada magunguna sun hada maganin rigakafin zazzabin cizon sauro ta farko a duniya.
A jawabin da yayi a lokacin da ya ke sanar da wannan nasara da aka samu shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya ce maganin zai taimaka wajen kare rayukan mutane musamman kananan yara daga kamuwa da cutar.
Abubuwa 10 da ya kamata a sani game da maganin rigakafin zazzabin cizon sauro.
1. Ruwan maganin rigakafin da aka hada na kai farmaki kan kwayar cutar mai hadari da aka fi samu a Afirka wato Plasmodium falciparum.
2. Ya kan yi kokari wajen yi wa kwayoyin cutar lahani jim kadan bayan shigarsu cikin jinin wanda sauraon ya ciza, ta hanyar toshe duk wasu kafofin shiga cikin kwayoyin halittar mutum.
3.Ana bukatar ayi rigakafin sau hudu. Za a iya yi wa yaro mai shekara 5 zuwa watanni 17 allurar rigakafin cutar sau uku sannan ayi wa yaro na karbi na huku din bayan watanni 18.
4. Kananan yara ne suka fi kasancewa cikin hadarin mutuwa daga cutar zazzabin cizon sauro.
5. Kafin kungiyar WHO ta amince da magani sai da aka tabbatar da ingancin maganin a kasashen Kenya, Malawi da Ghana.
6. Maganin na da ingancin samar da Kashi 30% na kariya daga kamuwa da cutar sannan ingancin maganin na saurin warwarewa a jikin mutum.
7. Idan aka fara amfani da maganin musamman a yankin Kudu da Sharan Afrika za a samu nasara wajen samar wa mutum miliyan 5.4 daga kamuwa da cutar sannan da dakile mutuwar yara ‘yan ƙasa da shekara biyar akalla 23,000.
8. Ba a cika samun matsaloli ba bayan an yi allurar rigakafin amma wasu lokutan akan yi fama da zazzabi.
9. An dana wannan magani daga sinadarin ‘Chile’ da aka gano daga bishiyar ‘Quillay’.
10. Gidauniyar Bill da Melinda gates, Gavi, the Vaccine Alliance, the Global Fund to Fight AIDS, Tuberculosis da Malaria ne kungiyoyin da suka samar da kudaden da aka yi amfani da su wajen aikin hada wannan maganin rigakafi.
Discussion about this post