Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, ya bayyana cewa umarnin da EFCC ta bai wa shugabannin bankuna ƙasar nan da manyan ma’aikatan bankuna cewa kowa ya bayyana kadarorin sa, ba bi-ta-da-ƙulli ba ne.
Bawa ya bayyana cewa an shigo da tsarin ne domin a tsaftace harkoki da hanyoyin hada-hadar bankuna.
Bawa ya yi wannan ƙarin haske a lokacin da ya ke jawabi a wani taron da Hukumar NDIC ta shirya wa jami’an tsaro a Abeakuta, babban birnin Jihar Ogun.
An shirya taron bitar ce a kan Hanyoyin Gudanar da Cikakken Bincike da Gurfanar da masu laifin harƙalla a bankuna.
Idan ba a manta ba, tun cikin watan Maris ne EFCC ta umarci manyan ma’aikatan bankuna a ƙasar nan su tabbatar sun bayyana ilahirin dukiyoyin da su ka mallaka, zuwa watan Yuni 1 Ga wata.
EFCC ta kafa dalilin ta na karɓar tilasta bayyana kadarorin, inda Hukumar ta kafa hujja da Dokar Najeriya ta 1986.
Ya ce yin ƙarin hasken ya zama dole, domin yawancin mutane sun jahilci abin da ake kira ‘bi-ta-da-ƙulli.
Haka nan kuma idan za a iya tunawa, cikin watan Yuli EFCC ta buɗe manhajar da za a riƙa kwarmata mata inda kadarorin ɓarayin gwamnati su ke.
Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa ya ƙaddamar da buɗe sabuwar manhaja, wato ‘app’ wanda jami’a za su riƙa shi ga a sauƙaƙe su na tura kwarmaton yadda ɓarayin gwamnati da ‘yan harƙalla ke karkatar da kuɗaɗen da su ka wawura.
Da ya ke wa ‘yan jarida ƙarin harke ranar Laraba yayin buɗe manhajar, Bawa ya ce ita ce irin ta ta farko a ko’ina.
Ya ce babban tasirin tsarin manhaja ɗin mai suna The Eagle Eye, wato Idon Mikiya a Hausance, shi ne sauƙin amfanin da manhajar ke gare ta, yadda ko daga gida da wayar hannu mutum zai iya amfani kai tsaye ya tura wa EFCC kwarmaton inda aka karkatar da wasu kuɗaɗe ko kadarorin harƙalla.
Abu na biyu kuma ya ce wannan hanya ba ta bukatar bayyana sunan wanda ya aika da kwarmaton, domin ita ma EFCC hujja kaɗai ta ke nema, ba ganin mutum ido-da-ido ba.
Ya yi kiran jama’a musamman ‘yan jarida wajen taya EFCC yaƙi da cin hanci da rashawa, ta hanyar yin amfani da manhajar The Eagle Eye su na kwarmata wa EFC bayanan harƙallar kuɗaɗen sata ko wata cuwa-cuwa.
“Babu ruwan ka da tashi sai ka je EFCC ka kai takardun bayanan ƙorafin wasu da su ka ɗirka cuwa-cuwa. Da ka shiga ‘app’, za ka iya tura wa wannan hukuma dukkan wasu bayanan da ka bankaɗo.
“Ko wani kantamemen gida ko rukunin gidaje ko maka-makan ginin zamani ka gani kuma ka san ba da gumin goshi aka tara kuɗaɗe ba, sai ka ɗauki hoton gidan ko ginin kawai ka shiga manhajar Eagle Eye ka tura wa EFCC.” Inji Bawa.