Shugaban Kasa Muhammadu Buhari gargadi masu bijiro da kamfen din tazarce bayan 2023 da su daina kuma su shiga taitayin su domin babu haka a tsarin sa.
” Da Al’kur’ani na yi rantsuwa kuma shekara hudu sau biya duka sai da na yi rantsuwa cewa iya shekarun da zan yi kenan, saboda haka kada wani ya bijiro da abinda bashi cikin kundin tsarin mulkin kasar nan. Ba zan lamince duk wanda ya bijiro da haka ba.”
Idan ba a manta ba shahararren mawakin Buhari da APC Rarara ya bayyana cewa a ra’ayin sa zai so a ce an kara wa Buhari shekaru 4 ko 5 bayan 2023 domin ya kammala wasu ayyuka da ya sa a gaba na ci gaban kasa.
Rarara ya fadi haka ne a hira da yayi da BBC Hausa.
Sai dai kuma shugaba Buhari ya gargadi masu kokarin bijiro da kamfen din ya zarce bayan 2023.
A takarda wanda kakakin fadar shugaban kasa Garba Shehu ya fitar ranar Juma’a ya bayyana cewa shugaba Buhari ya gargadi masu kokarin bijiro da haka.
” Kowa ya san nasarorin da muka samu musamman a wajen harkar tsaro a yankunan Arewa Maso Gabas da Kudu Maso Kudu. Yanzu yankin Arewa Maso Yamma ne ke ci mana tuwo a kwarya. Amma kuma kashin su ya kusa bushewa. Suna bi suna sace-sace da kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba.
Buhari ya ci gaba da cewa a cikin watanni 18 din da suka rage masa, zai ci gaba da ayyukan bunkasa tattalin arzikin kasa da samar da tsara da kuma samun ci gaba mai dorewa.
Wadannan sune kalaman da Buhari yayi a wajen kwarya-kwaryar ganawa da ‘yan Najeriya mazauna Saudiyya.
Buhari ya ziyarci kasar Saudiya domin yin aikin Umra da kuma ziyarar aiki.
Discussion about this post