Jigon jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya bayyana cewa ya fauwala wa Allah dangane da shugabancin Najeriya. Ya ce Allah ke bada mulki ga wanda ya ke so ya ba, ba wani ke bada mulki ba.
Tinubu ya yi wannan tawakkali a wuri taron gangamin yi masa maraba lale daga dawowa jiyyar da ya yi, bayan ya shafe watanni uku a tsakanin Amurka da Ingila.
Gwamnan Jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ne ya shirya gagarumin taron yi wa Tinubu addu’a.
Halartar taron dai shi ne fitar jigon na APC ta farko a cikin jama’a, tun bayan dawowar sa.
Dubban masoya, magoya baya da ‘yan jagaliyar siyasa ne su ka halarci gangamin a Lagos.
Tinubu ya ce ya yi murna kuma ya cika da mamakin ganin yadda aka taru a wurin domin yi masa addu’a.
Haka nan kuma ya nuna al’ajabin ganin yadda ɗimbin ‘yan Najeriya su ka riƙa yi masa addu’a da nuna alhini a lokacin da ya ke zaman murmurewa a London.
Shugaba Muhammadu Buhari, Sanata Lawan, Kakakin Majalisar Tarayya da ɗimbin sanatoci da mambobin tarayya sun riƙa yin karakainar zuwa duniyar Tinubu a Landan.
Haka su ma Gwamnonin Kudu Maso Yamma sun je dubiyar sa.
Tinubu ya daɗe ya na ƙwaƙwa da kwaɗayin zama shugaban ƙasa. Amma maitar sa ta ƙara fitowa fili a wanann zango na biyu na mulkin shugaba Buhari.
Akwai masu ganin cewa ta yiwu shi za a tsayar a takarar shugabancin Najeriya ƙarƙashin APC a zaɓen 2023.
Sai dai kuma wata ƙungiya ta tashi haiƙan ta na tallata Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo. Haka kuma Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi ya na ta karkarwar ƙoƙarin ɗaura zaren shiga damben takardar shugabancin ƙasa shi ma.