Yan Bindiga sun saki wasu daga cikin daliban kwalejin makarantar Gwamnatin Tarayya dake aYawurin Birnin Kebbi yau Alhamis.
Jaridar PREMIUM TIMES ta rawaito yadda Yan Bindigar suka arce da daliban a ranar 17 na watan Yuli a harabar makarantar dake a garin Yauri.
Yahaya Sarki, Kakakin gwamna Atiku Bagudu shi ne ya tabbatar wa manema labarai sakin daliban a yammacin Alhamis sai dai yace wasu ne daga cikin daliban aka sako kuma gwamnati tana kokarin ganin cewa an sako sauran daliban.
A yanzu daliban sun iso Babban Birnin Kebbi, kuma ana kokarin duba lafiyarsu kafin daga bisane a sadasu da iyalinsu.
Discussion about this post