Duk da dai har yau Shugaba Buhari bai fito ya bayyana ƴan bindiga cewa su ma ‘yan ta’adda ne kamar yadda ake kiran ƴan Boko Haram ba, a ranar Lahadi ya bayyana cewa “a wani ɓangaren ‘yan bindiga ba su da wani bambanci da ‘yan Boko Haram.”
Kakakin Yaɗa Labarai na Shugaba Buhari, Garba Shehu ne ya bayyana haka, a ranar Lahadi, bayan da wata mujalla mai suna The Economist, wadda ake bugawa a Landan ta buga labari cewa rashin tsaro a Najeriya ya ƙara dagulewa a ƙarƙashin mulkin Buhari.
‘Yan bindigar dai yanzu sun yi ƙarfin da har sun kai ga harbo jirgin yaƙin Najeriya ɗaya. Waɗanda Shehu ya ce sun yi ƙarfin tara kuɗaɗe da muggan makamai. “Kenan a nan ba su da wani bambanci ma da Boko Haram, waɗanda su a yanzu ma an yi masu tara-tara, an matse su a wuri ɗaya.”
‘Yan Najeriya da dama ciki har da Majalisar Dattawa da Gwamna El-Rufai na Kaduna, duk sun yi kira ga Buhari ya kira ‘yan bindiga cewa ‘yan ta’adda ne.
A martanin da Shehu ya yi masu, ya amince akwai ƙalubale daban-daban kan matsalolin tsaro a sassan ƙasar nan daban-daban.
Sai dai kuma ya ce duk Shugaba Buhari ya na ta ƙoƙarin magance matsalolin.
“Mujallar The Economist ta yi gaskiya, Najeriya na fuskantar matsalolin tsaro da dama. Sai dai a lura ba a cikin wannan gwamnatin matsalolin su ka faru ba. Wannan gwamnatin ce ma ke ta ƙoƙarin magance waɗannan ɗimbin matsalolin. “Alhali gwamnatocin baya babu wadda ta yi ƙoƙarin magance ko da matsala guda tal.” Inji Garba Shehu, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, kuma ya aiko wa PREMIUM TIMES.