Gwamnan Jihar Neja, Abubakar Bello, ya soke zaben sabon sarkin Kontagora saboda zargin aikata ba daidai ba a lokaci zabe daya gudana a ranar Alhamis a garin na Kontagora.
Gwamnan ya dauki matakin ne bayan takardar korafi da wasu ‘yan takarar su 46 masu neman sarautar Sarkin Sudan suka rubuta masa, suna nuna rashin gamsuwarsu da tsarin da wakilin gwamnati ya bi wajen yin zaben.
Yan takarar sun nemi gwamna ya gaggauta soke zaben, da kuma cire kwamishinan kananan hukumomi da masarautun gargajiya Abdulmalik Sarkin-Daji, saboda zargin kitsa murdiya a lokacin zaben.
Dama har an sanar cewa, wani Dan Kasuwa, mazaunin Kaduna, Muhammadu Barau-Mu’azu, shi ne yayi nasara bayan da masu zaben sarki suka zabe shi, a cewar kwamishinan kananan hukumomin a wata sanarwa da yayi a gidan Radio a Kontagora.
Amma, Barista Mika Anache, a cikin wata dogowar takardar korafi da ya rubuta wa gwamna da Jami’an tsaro, amadadin sauran Yan takara, yace anyi murdiya wajen zaben kuma ba’a gayyace suba wajen harkar zaben duk da cewa doka ta ce ayi komai a bayyane babu kumbiya-Kumbiya.
Bayan takardar korafi, Gwamna Bello, ta hannun sakataren Gwannatin Jiha, Ahmad Matane, ya bada sanarwar soke zaben cikin gaggawa da kuma canzawa kwamishinan kananan hukumomin wajen aiki.
Sanarwar yace Gwamna Bello yayi hakan ne domin ya tabbatar wa al’ummar Jihar cewa gwamnatinsa bata da wane Dan Takara da take goyan baya sai wanda mutane suke so kuma zatayiwa kowa adalci ta hanyar zabe mai inganci.
Sanarwar tace Emmanuel Umar ya maye gurbin kwamishinan kananan hukumomin Abdulmalik Sarkin-Daji, wanda shi ne zai gudanar da sabon zaben sarkin Sudan nan gaba kadan.
Marigayi Sarkin Sudan, Sa’idu Namaska, ya rasu ranar Alhamis din ta ta gabata bayan shafe shekaru 47 yana mulkin Kontagora.
Ya rasu yana da shekaru 84.