ZARGIN KWARTANCI: Yadda miji da mata su ka tona wa juna asiri a kotu

0

Wata mata mai suna Chima Udeni, ta zargi mijin ta da laifin neman ƙanwar ta da wasu daga cikin ƙawayen ta.

Chima ta yi wannan zargin a gaban Alƙalin Kotun Gargajiya ta Igandu da ke Lagos.

Tun da farko dai mijin ne ya maka ta ƙara kotun, inda ya nemi a raba auren na su bayan sun shafe shekaru 33 su na tare.

“Mata ta neman maza ta ke yi fafur. Har bari na ta taɓa yi da ‘ya’yan mu bakwai, ta tafi ta tare wurin wani farkar ta, ɗan asalin ƙauyen su.

“Da ta rabu da ni, sai da ta shafe shekaru 10 sannan ta dawo min cikin 2020.”

Haka mijin mai suna Tobechukwu ya shaida wa kotu.

Yayin da ta ke jawabi, Chima ta ce ai mijin shi ne tantagaryar manemin mata, domin ba ya da aikin komai sai lalata da ƙanuwar ta da kuma wasu ƙawayen ta.

“Ba shi da komai, ba ya ciyar da ni kuma ba ya ciyar da yaran mu. Duk ni ke ɗaukar ɗawainiyar ciyar da su.

“Gidan da mu ke zaune ni na gina shi. Ni ke ciyar da shi. Hatta ruwan da ya ke sha, Ni ke shayar da shi ruwan.

“Ya yi watsi da ni ya tare wajen wata farkar sa. Sannan kuma ya maida ƙanuwa ta da wasu ƙawaye na farkan sa, ya na lalata da su.

“Saboda haka tunda rabuwa ya ke so mu yi, ni ma hakan na ke so. Amma ya tashi ya bar min gida na. Ya tafi duk inda ya ke so.

“Idan na riga shi mutuwa, kada ya je jana’iza ta. Ni ma idan ya riga ni mutuwa, ko hanyar wurin da za a yi jana’izar sa ba zan bi ba.” Inji ta.

Mai Shari’a Adeniyi Koledoye ya roƙi su sulhunta juna, kuma su koma kotu ranar 21 Ga Satumba domin a sasanta su, idan har hakan zai yiwu.

Share.

game da Author