Gwamnatin Amurka ta taso dakataccen ɗan sandan Najeriya, Abba Kyari gadan-gadan a gaba, domin ganin an damƙa mata shi ta hukunta shi.
Kwanan nan mahukuntan ƙasar su ka kammala tattara hujjoji a kan zargin sa da aikata laifi, har tulin shafuka 2,7,07 a matsayin wani ɓangare na gabatar wa kotu da hujjojin cewa Kyari ya haɗa baki da ‘yan damfara, su Ramon Azeez, wanda aka fi sani da Hushpuppi, su ka damfari wani Balaraben Qatar Dalar Amurka miliyan 1.1, kuɗin da sun haura Naira miliyan 500.
Sauran wasu tulin hujjojin da ‘yan sandan na Amurka su ka tattara, sun haɗa har da maganganu da rubutattun saƙonni da tulin hotunan da gaba ɗaya nauyin su ya kai data 2.31.
Masu gabatar da ƙara a Amurka da su ma waɗanda ake tuhumar su uku sun amince a ɗaga shari’ar da watan Oktoba 2021 zuwa watan Mayu, 2022, domin kowane ɓangare ya ƙara kimtsawa.
Masu gabatar da ƙara sun nemi a tura shari’ar gaba, domin su samu wadataccen lokacin gabatar da ƙarin hujjoji ciki har da wasu da aka samu daga ƙasashen waje.
Akasarin hujjojin da su ka kai na nauyin data 2.31 GB da masu gabatar da ƙara a Amurka su ka ƙara samu, duk saƙonnin bayanai ne da su ka riƙa shiga da fita tsakanin lambar wayar Abba Kyari da Hushpuppi ta WhatsApp.
Sannan kuma akwai maganganun da jami’an tsaro su ka cac-cafko a wayar iska, waɗanda aka riƙa yi tsakanin Abba Kyari da su Hushpuppi.
Sannan kuma sun bayyana cewa nan da makonni biyu za su gabatar wa kotu da wasu hujjoji har shafuka 6,773 nan da makonni biyu.
Ana zargin su Abba Kyari da:
1. Haɗa gungun ‘yan damfara domin su aikata damfara.
2. Hannu dumu-dumu wajen karkatar da kuɗaɗe.
3. Satar kuɗaɗe tuburan-muraran.
A yanzu dai za a fara shari’ar mutum uku da ke tsare a Amurka. Shi kuma Abba Kyari da wasu mutum biyu mahukuntan Amurka na cigiyar su.
Waɗanda ke tsare a kurkukun Amurka, amma an bada belin su, mutum uku ne ‘yan Najeriya, amma mazauna can.
Sun haɗa da Rukayat Fashola, Bilatito Agbabiaka, sai Yusuf Anifowoshe. Amma an bayar da belin su, kuma ba su da hanyar guduwa daga Amurka.
Antoni Janar na Riƙo a Amurka Khaldoun Shobaki ne ya sa wa takardar amincewar a fara shari’ar cikin Mayu 2022.
Lauyoyin waɗanda ake zargin sun haɗa da Edward Robinson, Daniel Nardoni, sai kuma Lakeshia Monique Dorsey.
Sauran waɗanda mahukuntan Amurka ke ƙoƙarin kamuwa sun haɗa da Abba Kyari, Abdulrahman Juma da kuma Kelly Chibuzo Vincent.
Abba Kyari ya shiga wannan tsomomuwar da ta kai aka dakatar da shi kuma aka kafa masa kwamitin bincike, bayan an same shi da harƙallar kama Chibuzo ya tsare, tsakanin Nuwamba 2019 zuwa Afrilu 2020.
Kyari dai an zarge shi da haɗa baki da Hushpuppi ya kama Chibuzo ya tsare, har Hushpuppi ya yi nasarar damfarar Balaraben Qatar.
Hushpuppi ya sa Kyari ya tsare Chibuzo don kada ta gulmata wa Balaraben cewa damfara ce aka shirya za a yi masa.
An tsare Chibuzo saboda ya raina kuɗin da Hushpuppi ya ba shi matsayin kafin-alƙalwmin damfarar da aka fara karɓa a hannun Balaraben.
A kan haka ne ya ji haushi ya yi barazanar zai tayar da ballin komai. Shi ne Hushpuppi ya sa Kyari ya tsare shi, yadda ba zai samu damar kiran Balaraben a waya ba.
A ƙoƙarin da Kyari ya yi na wanke kan sa a shafin sa na Facebook bayan da asiri ya tonu, Kyari da kan sa ya yi iƙirarin cewa bayan ya tsare Chibuzo, ya gano cewa ba kashe iyalan Hushpuppi ya yi barazanar yi ba, kamar yadda Hushpuppi ɗin ya sanar da shi.
Kyari ya rubuta cewa ya gano Hushpuppi da Chibuzo abokan harƙalla ne, kuma saɓanin harƙalla ce ta sa Hushpuppi ya sa shi tsare Chibuzo.
Sai dai kuma bayan gano wannan ƙarambosuwa, maimakon Kyari ya rubuta rahoton neman a kamo Hushpuppi shi ma saboda ɗan damfara ne, sai Kyari ɗin ya riƙa mu’amala da shi, har guza ya koma abokin damo.
Discussion about this post