Gwamnatin jihar Zamfara karkashin gwamna Bello Matawalle ta rufe makarantun jihar gaba daya saboda tsananin hare-hare da ya dirkako jihar.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ‘Yan bindiga suka afka makarantar sakandaren gwamnati dake Maradun, suka sace daliban makaranta 76 kamar yadda gwamnati ta sanara da rana tsaka ran Laraba.
Maradun ita ce mahaifar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle.
Wasu mazauna garin sun shaida wa wakilin PREMIUM TIMES cewa maharan sun dira makarantar da rana tsaka inda suka kwashi na kwasa wasu kuma cikin dalibai da malaman makarantar suka arce.
Wasu daga cikin malamai da daliban da suka arce sun saida mana cewa suma ba su san ko dalibai nawa bane maharan suka sace.
Wani jami’in gwamnati ya tabbatar mana cewa lallai mahara sun sace dalibai kuma suna ganawa da jami’an tsaro a yanzu haka. nan bada dadewa ba zasu fidda sanarwa akai.
Jihar Zamfara kamar wasu jihohin Arewacin Najeriya na ci gaba da fama da hare haren ‘yan bindiga da yasa jiha kamar ta Kaduna har yanzu basu yarda yaran makaranta sun koma ajujuwa ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar , Ayuba Elkana ya sanara da saka dokar hana walwala daga karfe 6 na dare zuwa 6 na safe a kananan hukumomi 13, sannan karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe a garin Gusau.
Discussion about this post