Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya jinjina wa mutanen jihar Kaduna kan nasarar da jihar ta samu a lokacin da ta gudanar da zabukan Kananan hukumomi a karshen makon jiya.
El-Rufai ya bayyana haka da wasu nasarorin da jihar ta samu a wannan zaɓe a jawabi da yayi wa mutanen jihar ranar Laraba.
” Ya zama dole in fito in jinjina wa mutanen Kaduna domin sun ba maraɗa kunya a wannan zabe. Baya ga zabe da aka yi cikin kwanciyar hankali da lumana, an yi shi cikin natsuwa da gaskiya kurukuru kowa ya shaida.
” An yi amfani da na’urar zabe kuma zaɓe yayi kyau matuka, babu cuta babu cutarwa. Sannan wani abin farin ciki shine yadda mutane suka yi na’am da na’urar. Komai yayi kyau, mashaAllah.
” Wani abinda ya daɗa faranta min rai shine yadda jam’iyyar APC ta samu karbuwa a yankin kudancin Kaduna. Baya ga yin nasara da ta yi a kananan hukumomin da a baya ke karkashin ikon ta ta samu karin wasu ƙananan hukumomin har guda uku.
” Baya ga samun nasara a kananan hukumomin da dama na APC ne, wato kananan hukumomin Sanga da Kagarko, APC ce ta yi nasara a Kauru da Jema’a. Wannan ya nuna cewa jam’iyyar ta fara kwanciya wa mutanen yankin Kudancin Kaduna.
Baya ga nasarar da ta samu a waɗannan kananan hukumomi, babu wata karamar hukuma wanda mahaifar wani jigon PDP ce da APC ba ta lashe shi ba a Arewacin Jihar.
Discussion about this post