YUNWA BA AI MAKI ‘LA HAULA’: Gwamnatin Tarayya ta fara koya wa manoman Arewa maso Yamma dabarun noman rogo

0

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin bayar da horon dabarun noman rogo ga manoman yankin Arewa maso Yamma.

Shirin wanda aka fara a ranar Alhamis an bijiro da shi ne a yankin domin a cike wawakeken giɓin da ake fama da shi wajen kasa samar da wadataccen rogo a yankin.

Ma’aikatar Gona ta Tarayya ce ta bijiro da shirin, wanda aka ƙaddamar a Birnin Kebbi, domin a nuna wa ɗimbin manoma yadda ake samun alfanu daga noman rogo, tare da samun rogon a wadace ta hanyar bunƙasa noman sa.

Darakta a Ma’aikatar Harkokin Noma, Karina Babangida, ta bayyana cewa duk da yawan rogon da ake nomawa a Najeriya bai ma kai metrik tan 10 a duk hekta ɗaya ba, amma kuma har yanzu Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace ƙasa noman rogo mai yawa a duniya.

Mataimakin Darakta Hakeem Raji ne ya wakilci Karima Babangida a wurin ƙaddamar da shirin, inda ya ce Najeriya za ta iya noma rogo metrik tan 40 a duk hekta ɗaya, amma idan manoman rogon su ka rungumi tsarin noman da ya dace su runguma domin bunƙasa noman rogo.

Hanyoyin da ya ce za su runguma kuwa, sun haɗa da amfani da kayan noma na zamani, sannan kuma su inganta dabarun dashen rogo.

“Ɗaya daga cikin muhimman abin da wannan gwamnati ta fi maida hankali shi ne Bunƙasa Harkokin Noma (Agriculi Promotion Policy), wato tsarin fatattakar yunwa baki ɗaya daga Najeriya. Wannan hanya kuwa ita ce ta samar da hanyoyi da dabarun noma masu sauƙi ga manoman karkara.

“Idan aka yi la’akari da yadda rogo ya ke da muhimmanci ga rayuwar al’umma wajen samar da abinci a sauƙaƙe, har sauran kayayyakin da su ka shafi magunguna da sauran su, to noman rogo wadatacce zai zama alfanu a cikin al’ummar ƙasar nan.”

Share.

game da Author