Najeriya na bin kamfanonin hada-hadar fetur da gas bashin dala biliyan 6.8, kwatankwacin Naira tiriliyan 2.6.
Babban Sakataren NEITI, Orji Ogbonnaya ne bayyana haka, a ranar Talata.
Ya ce basussukan da Najeriya ke bin kamfanonin sun samo asali ne daga ƙin biyan harajin ribar da su ke samu, ƙin biyan harajin ilimi, ƙin biyan VAT, da sauran harajin da su ka haɗa har da kuɗaɗen ladar aro.
Sai dai kuma Ogbonnaya bai ambaci sunayen kamfanonin ba.
Da ya ke zantawa da manema labarai, Ogbonnaya ya ci gaba da cewa NEITI ta gano wannan tulin maƙudan kuɗaɗen bashi da Najeriya ke bin kamfanonin, amma sun ƙi biya tun a cikin bin-diddigin da hukumar ta yi a cikin 2019 a fannin harkokin fetur da gas.
Ya ce idan da za a iya biya ko iya karɓar kuɗaɗen a yanzu, za a iya amfani da su wajen gudanar da ayyukan da ake ta haƙilon neman bashin da za a yi ayyukan a cikin kasafin 2021.
Gwamnatin Buhari ta karɓo bashi daga wurare daban-daban har na sama da Naira tiriliyan 5 domin cike giɓin kasafin kudi.
Na baya-bayan nan shi ne shi ne wanda ta karɓo na Naira biliyan 5 da kuma na Naira biliyan 4 a makon da ya gabata.
Ogbonnaya ya ce kamfanonin fetur da gas sun riƙe wa Najeriya dala miliyan 143.99, sai kuma bashin dala biliyan 1.089 na ribar fetur da har yau ba su biya ba na harajin kamfanoni.
Akwai kuma wasu bashin dala miliyan 201.69 na harajin fannin ilmi da har yau ba su biya Najeriya ba.
Ogbonnaya ya ci gaba da bayar da adadin sauran nau’ukan basussukan da Najeriya ke bin kamfanonin su 77, waɗanda ya ce ya kamata a karɓo kuɗaɗen domin a samu yin ayyukan raya ƙasa da su a cikin Najeriya.
Ya ce kuɗaɗen sun isa a aiwatar da ayyukan kasafin kuɗin Najeriya na 2020 da su.
A ƙarshe ya yi kiran a fara shirin karɓo kuɗaɗen, ta hanyar kafa wani gagarumin kwamitin karɓo basussukan.