A yanzu haka akwai ƙudirori fiye da 200 a Majalisar Tarayya jibge, na waɗanda su ka gabatar da buƙatar a gina jami’o’i da manyan makarantun gaba da sakandare a mazaɓun su.
Akwai jami’o’i 98 na gwamnati a Najeriya, waɗanda a kullum su ke kwana su na tashi cikin matsalar ƙarancin kuɗaɗen gudanarwa daga gwmnati, yawan yajin aikin malamai da makaranta a kan matsalar biyan albashi da alawus-alawus.
Masana sun danganta waɗannan matsaloli na rashin bayar da kuɗaɗe ga jami’o’in Najeriya sun taimaka wajen mayar da harkar ilmi koma-baya a tsakanin jami’o’in duniya.
Taɓarɓarewar ilmi a Najeriya ya yi lalacewar da babu jami’ar Najeriya ko guda ɗaya a cikin jami’o’i nagari fitattu 1,000 a duniya.
Hausawa na cewa abin da ya ci Doma, ba ya barin Awai. Irin matsalar da ta addabi jami’o’i 98 na ƙasar nan, iri daya ne da waɗanda su ka dabaibaye Kwalejojin Fasaha da Manyan Kwalejojin Ilimi 120 da ake da su a ƙasar nan.
Sai dai kuma duk da wannan mawuyacin halin da manyan makarantu ke ciki, a yanzu haka akwai ƙudirori na neman kafa jami’o’i da manyan makarantu fiye da 200, waɗanda ‘yan Majalisar Tarayya ke neman a kafa a mazaɓun su.
Akasarin waɗannan masu neman a kafa makarantu a yankin su, duk batu ne na siyasa kawai ba wani lamari na kishin bunƙasa harkokin ilmi ba.
Shekaru 11 bayan yarjejeniyar da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) ta yi da Gwmnatin Tarayya, inda Gwmnatin Tarayya ta yi alƙawarin ƙara dumbuza kuɗaɗe domin bunƙasa ilimi, har yau ASSU ba ta daina yawan tafiya yajin aiki saboda kuɗi ba.
Daga cikin dalilan kuwa, saboda har yau gwamnati ba ta iya cika alƙawurran da ta ɗauka ba na biyan buƙatun ASUU.
Duk da wannan hali da ake ciki, ‘yan majalisar tarayya sai gasar gabatar da ƙudirin neman a kafa manyan makarantu a mazaɓun su su ke ta yi.
Ƙididdigar Hukumar Kula da Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) ta ce akwai jami’o’i mallakar gwamnatin tarayya guda 45 a ƙasar nan.
Sai kuma jami’o’i 53 mallakin jihohi daban-daban. Akwai kuma jami’o’i masu zaman kan su guda 99.
Sannan akwai Manyan Kwalejojin Ilimi na Tarayya 27 da kuma 49 na Gwamnatocin Jihohi daban-daban, kamar yadda Hukumar Kula da Manyan Kwalejojin Ilimi ta Ƙasa (NCCF) ta tabbatar.
Gaba ɗaya dai NCCF ta ce akwai makarantu da masu bayar da satifiket na NCE har guda 200 a Najeriya.
Samnan kuma akwai Kwalejojin Fasaha na Gwamnatin Tarayya (Federal Polytechnics) guda 32, wasu 51 mallakar gwamnatocin jihohi da kuma wasu 64 masu zaman kan su.
Duk da waɗannan, a yanzu akwai ƙudirori 126 a Majalisar Tarayya na masu so a kafa ƙarin jami’o’i. Akwai ƙudirori 140 na masu neman a kafa masu manyan kwalejoji da kuma 27 masu neman a kafa masu Kwalejojin Fasaha.
Akasari duk ‘yan majalisar da su ka bijiro da waɗannan ƙudirori, so su ke yi a kafa makarantun a mazaɓun su. Hakan ya sa ake wa lamarin kallon duk siyasa ce.