Dan majalisan dake wakiltan Sabon Birni a majalisar Dokokin jihar Sokoto, Saidu Ibrahim ya koka kan yadda ‘yan bindiga suka mamaye shiyyar Sokoto ta Gabas sai yadda suka yi da mutane ba tare da fargabar jami’an tsaro ba.
Saidu ya ce bashi da halin ziyartar gida yanzu saboda ‘yan bindiga.
” Ba zan iya zuwa ganin gida ba saboda ‘yan bindiga sun mamaye garuruwan mu kaf. Za ka ga sojoji amma a cikin garin Sabon Birni amma kuma kauyukan da ke zagaye da manyan garuruwan da sosojin ke sintiri ciki suke da ‘yan bidiga suna yin abin da suka ga dama.
” Idan jami’an tsaro ba su san inda suke bane, ni dinnan na yi alkawarin zan shiga gaba muje kauyukan da suka kakagida in nuna musu ‘yan bindigan idan ma ba su san inda suke bane.
” Wannan tashin hankali har ina, mutanen nan sun shigo mana kasa suna kisa son ran su sannan suna kwashe jama’a. Abin fa ya kazanta sosai.
Discussion about this post