Wani Mazaunin garin gangara dake jihar Sokoto ya tabbatar wa wakilin mu cewa mutane da ba a san adadin su ba ne yan bindiga suka kashe kuma suka sace a harin da suka kawo kauyen gangara ranar Talata.
Kakale wanda mazaunin kauyen gangara ne ya bayyana cewa maharan masu yawa sun shigo garin dauke da bindigogo suka rika dirka wa duk wanda suka ci karo da, babu yaro babu babba har da mata.
” Bayan ciccinawa shaguna da gidajen mutane wuta da suka yi, sun rika shiga cikin gidajen mutane daya bayan daya suna harbin mata da yara da duk wanda suka ci karo da.
Kakale ya ce wasu da yawa sun arce zuwa garin Sabon Birni, wasu kuma sun fada cikin koramu da kududdufai garin gudu.
Wannan hari ya zo kwanaki kadan bayan gungun yan bindiga sun afkawa sansanin Sojoji a jihar Sokoto suka kashe sojoji da dama a harin bazata da suka kai musu.
Discussion about this post