‘Yan bindiga sun afka makarantar sakandaren gwamnati dake Maradun, sun sace daliban makaranta da ba a san yawan su ba da rana tsaka.
Maradun ita ce mahaifar gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle.
Wasu mazauna garin sun shaida wa wakilin PREMIUM TIMES cewa maharan sun dira makarantar da rana tsaka inda suka kwashi na kwasa wasu kuma cikin dalibai da malaman makarantar suka arce.
Wasu daga cikin malamai da daliban da suka arce sun saida mana cewa suma ba su san ko dalibai nawa bane maharan suka sace.
Wani jami’in gwamnati ya tabbatar mana cewa lallai mahara sun sace dalibai kuma suna ganawa da jami’an tsaro a yanzu haka. nan bada dadewa ba zasu fidda sanarwa akai.
Jihar Zamfara kamar wasu jihohin Arewacin Najeriya na ci gaba da fama da hare haren ‘yan bindiga da yasa jiha kamar ta Kaduna har yanzu basu yarda yaran makaranta sun koma ajujuwa ba.
Discussion about this post