Gwamna Muhammad Badaru na Jihar Jigawa, a ranar Laraba, ya kori shugaban ma’aikatar fansho, Hashimu Fagam.
Gwamna Badaru ya kuma amince da nadin Kamilu Musa a matsayin sabon shugaba a humumar ta fansho.
Gwamnan bai bayyana dalilin da yasa ya sallami Hashimu ba.
Amma Jaridar PREMIUM TIMES HAUSA ta gano cewa korar tana da nasaba da wani zangazanga da Yan Jam’iyyar ta APC daga Gwaram sukayi a gidan gwamnati a Dutse.
Masu zangazangar sun nuna rashin amincewa da Shugabancin Jam’iyya a Karamar Humumar Gwaram wanda ake zargin gwamnan ne ya amince da Shugabancin domin masalahar Yan Jam’iyyar masu rikici da juna a yankin.
Ana zargin Hashimu, da Dan Majalissar dokokin ta Tarayya mai wakiltar Gwaram, Shitu Galambi, da daukar nauyin masu zangazangar zuwa Dutse.
Dukkaninsu su biyun Hashimu da Galambi suna adawa da Shugabancin Jam’iyyar a Karamar hukumar ta Gwaram kuma sunki yiwa gwamna biyayya.
Takardar korar Hashimu ta fito ne daga ofishin shugaban ma’aikatar Jihar, Hussaini Kila.
Yanzu dai baraka ta fito fili tsakanin gwamna Badaru da Shitu Galambi wanda a baya aka zargin gwamnan da yin kama karya wajen tabbatar da shi Galambi a matsayin dan takarar dan Majalissa.
Shin ko yanzu Badaru yayi nadama? lokaci ne kawai zai nuna hakan.
Discussion about this post