Kakakin rundunar ‘yan sanda Jigawa Lawan Shiisu ya bayyana wa ‘yan jarida cewa ‘yan sanda masu patrol cikin dare a Unguwar Kunnadi suka kama matashin mai shekaru 25.
” Yan sanda sun kama wannan matashi mai shekaru 25 ne a daidai yana aikata wannan abu. Ya kama wannan akuya ne da karfin tsiya sannan ya rika saka mazakutar sa a bayan wannan akuya har yan sandan suka kama shi turmi da tabarya.
Shiisu ya ce an fara gudanar da bincike a kai kuma da zarar an kammala binciken za a kai shi gabar kuliya.
Discussion about this post