Jami’ar Fasaha ta Tarayya da Gwamnatin Jigawa ta amince a kafa, ta na ɗaya daga cikin waɗanda Gwamnantin Tarayya ta bayyana sunayen su guda huɗu.
Guda huɗu ɗin sun haɗa da ta Jigawa, Akwa Ibom, Osun da kuma ta Jihar Bauchi.
Ministan Harkokin Ilmi, Adamu Adamu ne ya bayyana sunayen su tun a ranar 21 Ga Yuni, a Abuja, ta bakin Babban Sakataren Ma’aikatar Ilmi, Sonny Echono.
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa an kafa su ne domin a rage matsalar ƙarancin ɗaliban fasaha a fannin ilmi a Najeriya.
Haka kuma Ministan Ilmi ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince zai bayar da naira biliyan 4 ga kowace jami’ar Fasaha ɗin su huɗu, domin fara aiki gadan-gadan.
Ya ce za a ciri kuɗaɗen daga Gidauniyar TETFund.
An karɓi wannan sanarwa cikin murna a Jigawa, sai dai kuma abin da ya biyu baya, shi ne rigimar shiyyar da ya kamata a kafa jami’ar a Jigawa.
An dai ƙirƙiri Jigawa daga Jihar Kano a ranar 27 Ga Agusta, 1991, a ƙarƙashin mulkin Shugaba Ibrahim Babangida.
Jigawa na da ƙananan hukumoni 27, kuma ita ce jiha ta takwas wajen yawan jama’a a Najeriya.
Akwai Masarautu biyar a Jihar Jigawa. Kuma akwai Jami’ar Tarayya a Dutse babban birnin jihar. Sai masarautar Haɗeja, Gumel, Kazaure da kuma Ringim.
A Masarautar Haɗeja akwai Jami’ar Sule Lamiɗo a Kafin Hausa. Akwai kuma NOUN a Haɗeja da kuma jami’a mai zaman kan ta ta Assalam da ake ginawa yanzu haka a Haɗeja.
A Masarautar Kazaure akwai Federal Polytechnic a Kazaure da wasu manyan makarantu. Har da College of Education.
Haka Masarautar Gumel akwai Federal College of Education da wasu.
Bayyana sabuwar Jami’ar Fasaha ta Tarayya ke da wuya sai waɗannan Masarautu biyar su ka fara tayar da jijiyar wuya kowa na so a kafa ta a ɓangaren sa.
Cikin 2011 dai Shugaba Jonathan na lokacin ya kafa Jami’ar Tarayya a Dutse, wadda ke ɗaya daga cikin 12 ɗin da Jonathan ya kafa a ƙasar nan.
Ahmed Ilallah ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ce ta haifar da wannan ce-ce-ku-ce a Jihar Jigawa, saboda ba ta bayyana sunan garin da za a kafa jami’ar ba. Amma a jihar Bauchi ta bayyana cewa a Azare za a gina jami’ar.
“A duk Arewacin Najeriya, Masarautar Haɗeja ce kaɗai a Jigawa babu Jami’ar Gwamnantin Tarayya, duk kuwa da tarihin da ta ke da shi. Ko a zamanin da can, Gundumar Katagum a ƙarƙashin Haɗeja ta ke.”
Illallah ya roƙi Ministan Ilmi a kafa wannan sabuwar Jami’ar Fasaha ta Tarayya a Haɗeja.
Amma kuma tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Jigawa, Baffa Alasan na ganin cewa a Ringim ya dace a kafa jami’ar.
Ya kafa hujja da cewa har yau Shugaba Muhammadu Buhari bai kafa wani aikin raya ƙasa a Ringim ba. Don haka kafa jami’ar a can ya cancanta matuƙa.
Shi kuwa malami a College of Education Gumel, mai suna Rabiu Ibrahim, ya na ganin a kafa jami’ar a Masarautar Gumel shi ya fi cancanta.
Ya ƙara da cewa idan aka ce za a kafa ta a sabon wuri, to naira biliyan 4 fa ta yi kaɗan, musamman idan aka ce a cikin 2022 za a fara ɗaukar darussa
a cikin ta.
Shi kuwa Adamu Maiɗalibai na ganin a kafa ta a Kazaure shi zai fi komai sauƙi da kuma dacewa.
Sai dai a cikin watan Agusta Gwamnantin Jigawa ta bayyana cewa za a kafa jami’ar a Ɓaɓura, garin haihuwar Gwamna Abubakar Badaru na jihar.
Garin Ɓaɓura na ƙarƙashin Masarautar Ringim.
Kakakin Yaɗa Labarai na Gwamna Badaru, Habibu Kila, ya fitar da sanarwa cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kafa jami’ar a Ɓaɓura.
Discussion about this post