Hukumar NDLEA ta bayyana yadda ta kama muggan kwayoyi masu nauyin kilogiram 500 da masu safarae kwayoyin a jihohi 8 a kasar nan.
Kakakin hukumar Femi Babafemi ya sanar da haka a lokacin da ya ke hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ranar Lahadi a Abuja.
Babafemi ya ce daga ranar 30 ga Agusta zuwa 2 ga Satumba hukumar ta kama kwayoyi dake nauyin kilogiram 384.7 a Lokoja jihar Kogi za a kai su Abuja.
Hukumar ta kuma kama wata babban mota mai lamba AA462QAP jihar Filato dauke muggan kwayoyi da aka boye a cikin kwalaben abinci.
“An kama kwalaben maganin tari na codeine guda 1,975, kwayoyin Exol-5 guda 199, kwayoyin Diazepam guda 250, tabar wiwi da ya kai nauyi kilogiram 5.9, ruwan allurar Ketamine da ya kai nauyin kilogiram 378.7.
Direban dake tuka motar Danlami Dodo mai shekara 50 ya dauko muggan kwayoyin daga Onitsha jihar Anambra zuwa Abuja, jami’an NDLEA sun kama motar a Lokoja jihar Kogi.
Ya ce Babafemi ya ce hukumar ta kama mota kirarn Toyota Hiace bus dake lamba MUS716XK jihar Legas da kwayoyin Arizona da aka boye a cikin buhu aka saka su cikin kwalaye.
Motar ta taso daga Ojota daga jihar Legas zuwa Abuja.
A jihar Barno hukumar ta kama Caleb Okezuonu da kwalaben maganin tari na codeine guda 352 da kwayoyin maganin Rohypnol guda 876.