Majiya masu dama sun tabbatar cewa Bello Turji, ƙasurgumin ɗan bindiga da yayi kaurin suna a dazukan yankin Zamfara, Katsina da Sokoto ya kai hari sansanin sojoji a Sabon Birni.
Sai dai kuma majiyar ba su faɗi yawan sojojin da ƴan bindiga suka kashe a wannan hari da suka yi shi a tsanake.
Sai dai kuma ko da wakilin PREMIUM TIMES ya nemi ji daga bakin rundunar ƴan sanda, sun bayyana cewa har yanzu basu da labarin wannan hari.
Turji, mai shekaru 27, ba shi da mutunci da tausayi, sannan shine gogarman dazukan Zamfara da Sokoto. An yi mai tayin sulhu amma ya ki amincewa.
Sau ɗaya tal da ya amince a yi sulhu da shi, shine lokacin da Sheikh Gumi ya ziyarce shi a daji
Har yanzu Turji ya na tsare da mahaifi, kishiyar mahaifiya da kawun shugaban majalisar jihar Zamfara da wasu da dama.
Usman Tara wanda mazaunin Sokoto ne ya bayyana cewa ƴan bindiga sun afka wa wa sojojin ne da ke wani makarantar Firamare dake lauyen Dama, Sabon Birni inda maharan suka diran musu ba shiri.
” Tsakani da Allah yadda ƴan bindiga suke sheke ayar su a wannan yankin ya na matukar tada mana hankali sannan duk muna cikin tsoro da fargaba. Ace wai ƴan bindiga za su dira sansanin sojoji, su tafi da su, su kwashe makaman su da motocin su hankali kwanci, abin tsoro ne matuƙa a gare mu.
Shi ko Altine Bashir ya ce ” Bari in tabbatar muku cewa mutanen Turji sun zagaye makarantar da sojojin ke kwana ba su sani ba, daga nan sai suka buɗe musu wuta. Sun kashe wasu sojojin wasu kuma sun gudu cikin ƙauyen Nijar.
” Turji ya dawo da Hedikwatar sa Sokoto kuma yayi haka ne domin ya tsorata sojoji da kuma nuna isa ga jami’an tsaron Najeriya.