Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun, mataimakin gwamna Noimot Salako-Oyedele, da kakakin majalisar jihar Olakunle Oluomo, duk sun tattara sun koma can kasar Birtaniya, birnin Landan, dag can ne suke gudanar da ayyukan gwamnati.
Sai dai kuma shi kakaki Oluomo an ce kasar Amurka ya tafi taron majalisar Dinkin duniya.
Sai dai kuma kwamishinan yada labaran jihar Waheed Odusile ya bayyana cewa ba rashin lafiya bane ya kai gwamna Abiodun kasar Birtaniya, Lafiyan shi lau.
Ya kara da cewa gwamnan yana gudanar da ayyukan gwamnati daga can kasar Landan, sannan kuma kafin ya bar Najeriya ya fadi wa jami’an gwamnati abin da za su yi idan baya nan.
Lauyoyi da dama ciki har da tsohon mataimakin shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya Monday Ubani, sun ce abinda gwamna yayi karya doka ce domin doka ta bashi damar ya mika mulki ga mataiamakiyar sa ne idan zai dauki hutu ko kuma wata doguwar tafiya ta kama shi.