Ministan Tsaro Bashir Magashi ya bayyana cewa lallai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fusata kan yadda ƴan bindiga suke cin karen su ba babbaka a yankin Arewa Maso Yammacin Kasar nan.
Magashi ya ce Buhari ya umarci jami’an tsaron kasar su fantsama cikin dazukan da ƴan bindiga suke su gama da su, rashin mutuncin da suke yi ya ishe su haka.
” Wannan ganawa da muka yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari, an yi shi domin a yi masa filla-filla game da halin da ake ciki kan tsaro a Kasar nan da kuma yadda jami’an tsaro le tunkarar sa.
” An tattauna halin da ake ciki da kuma rashin mutuncin da ƴan bindiga ke yi wa mutane a yankunan jihar Zamfara da matsalar tsaro a yankin Arewa ta Tsakiya. Maharan na ganin sun riƙa, suna yin abinda suka ga dama. Suna ganin kamar sun fi karfin gwamnati a ƙasar nan ne. Sannan har maganganun banza suke yi suna babbanƙarewa suna ɗaga kafaɗu. Ya ishe su hakanan.
” Idan da mutane za su yi waiwaye kaɗan baya zuwa 2014, za su san cewa lallai wannan gwamnati, wato gwamnatin Buhari ta taka rawar gani matuƙa musamman a harkar tsaron kasar nan.
Magashi ya kara da cewa wannan shine saƙon da shugaba Buhari ya aike su su aikata kuma ba za su ba maraɗa kunya ba. ” Ya ce duk wata dabara ta aikin soja mu yi amfani da su mu tabbatar an kawo ƙarshen ƴan bindiga a wannan yanki.
Discussion about this post