TSANANIN RASHIN TSARO: Buhari ya ci amanar Katsinawa – Dan majalisar Katsina

0

Honorabul Aminu Garba dake wakiltar karamar hukumar Danmusa a majalisar jihar Katsina ya ya ragargaji shugaban kasa Muhammadu Buhari inda ya ce zabar sa da Katsinawa suka yi bai haifar musu da da mai ido ba.

” A Kauyen Marken Dambi dake karamar hukumar Danmusa, ko jiya sai da mahara suka kashe mutum daya suka sace mata da yarta. Jihar Katsina ce ta fi baiwa Buhari ‘madarar’ kuri’u a lokacin zabe amma kuma babu wani abu daya da za mu ce wai gashi mun amfana dashi ko su.

” Na gaya wa mutanen da nake wakilta cewa kowa ya tattara kayan sa ya yi hijira domin gaskiyar magana itace gwamnati ta gaza mun gaza, nima ba na iya zuwa garin Danmusa saboda azaba da tsananin rashin tsaro da ake fama da shi.

” Wannan sako da na aika wa mutane na, ban yi tantamar fadin sa ba saboda gaskiya ce na fadi kuma ba zan yi da na sani akai ba.

Share.

game da Author